Hazon gobarar daji na barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Indonesia
Tsawon makonni da dama, ƙasar Indonesia na fama da mummunar gobarar dazuka wadda ta haddasa yaɗuwar hayaƙi mai guba da ya rufe manyan sassa na ƙasar.
Miliyoyin mutane a yankunan Sumatra da Kalimantan sun kasance cikin haɗarin shaƙar gurɓatacciyar iska, inda dubban mutane tuni aka kwantar da su a asibitoci saboda cututtukan da suka shafi numfashi.
Hayaƙin da gobarar ta haifar ya kuma bazu zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Malaysia da Philippines, lamarin da ya jawo damuwa a faɗin yankin Kudu maso Gabashin Asiya.
A yau, za mu ci gaba da kawo muku sabbin bayanai kai tsaye daga yankunan da abin ya shafa, tare da bayyana yadda wannan hayaƙi mai guba ke taɓa rayuwar yau da kullum a wasu daga cikin manyan yankuna masu yawan jama'a a Kudu maso Gabashin Asiya.