Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 25/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 25/10/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Iran da ƙawayenta na shirin kai mana hari lokacin zaɓe - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce Iran da ƙawayenta na iya ƙoƙarin kai hare-hare domin kawo cikas ga zaɓen Isra'ila da za a gudanar ranar Talata.

    A cikin wani bidiyo da ofishinsa ya fitar a ranar Lahadi, Netanyahu ya ce:

    "Muna da bayanan sirri da ke nuna cewa maƙiyanmu, wato Iran da ƙawayenta, na iya ƙalubalantar mu ta hanyar kai hare-hare domin kawo cikas ga zaɓen."

    Netanyahu ya ci gaba da magana a cikin bidiyon, yana nuni da shirye-shiryen kariya da na kai farmaki na sojojin Isra'ila, inda ya yi gargaɗi da cewa:

    "Za ku ga buƙatarmu. Za ku sha mummunan martani wanda ya fi abin da kuke zato nesa."

    Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankali tsakanin Isra'ila da Iran, yayin da zaɓen Isra'ila ke kara gabatowa.

  2. An ji ƙarar fashewa a Riyadh yayin da aka sake buɗe filin jirgin saman Sarki Khalid

    An samu rahotannin jin ƙarar fashewa a babban birnin Saudiyya, Riyadh. Wannan na zuwa ne bayan da muka ruwaito cewa hukumomin Saudiyya sun sanar da cewa za a dawo da zirga-zirgar jiragen sama a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sarki Khalid daga yau Lahadi.

    An rufe filin jirgin na Sarki Khalid na tsawon makonni biyu bayan jerin hare-haren da mayakan Houthi suka kai akai-akai.

    Shafin Flightradar, wanda ke bibiyar zirga-zirgar jiragen sama a duniya, ya kuma ruwaito cewa wani jirgin sama ya tashi daga filin jirgin a farkon sa’o’in yau.

    Hukumar Saudiyya ba ta bayyana musabbabin sabon fashewar da aka ji a babban birnin ba.

    A halin da ake ciki, kakakin rundunar sojin Houthi, Yahya Saree, ya yi gargadin cewa filin jirgin har yanzu “ba shi da tsaro” kuma “har yanzu yana cikin jerin wuraren soji da ake kai wa hari.” Ya ce Saudiyya ce za ta ɗauki alhakin duk wani sakamako da zai biyo bayan sake buɗe filin jirgin.

    Mayakan Houthi sun kai hare-hare kan filin jirgin a lokuta da dama tun bayan rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta. Wani hari da aka kai a farkon wannan wata ya kashe mutum 13 tare da jikkata sama da mutum 300, wanda ya zama hari mafi muni da aka kai a Saudiyya cikin shekaru goma da suka gabata.

    Saudiyya, wadda ke jagorantar kawancen soji da ke yaƙi da Houthi, ta ci gaba da kai hare-hare kan yankunan da ƙungiyar ke iko da su a cikin makonnin baya-bayan nan.

  3. Babbar 'yar adawar Venezuela Maria Machado ta koma ƙasar bayan gudun hijira

    Shugabar adawar ƙasar Venezuela, María Corina Machado, ta koma gida cikin wani yanayi na siyasa mai cike da ƙalubale bayan fiye da watanni 10 da ta shafe a gudun hijira.

    A ranar Lahadi, Machado ta rubuta a shafinta na X cewa: "Ina nan. Tare da ku."

    Abokin gwagwarmayarta kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Edmundo González Urrutia, ya tabbatar da labarin mintuna kaɗan bayan haka, inda ya rubuta cewa: "Ina farin cikin sanar da ku cewa shugabarmu, ƙawata María Corina, tana kan ƙasar Venezuela."

    A watan Janairu, wata guda bayan da Machado ta bar Venezuela domin karɓar Lambar Yabo ta Nobel ta Zaman Lafiya a Norway, Amurka ta kama abokin hamayyarta, Shugaba Nicolás Maduro.

    Daga nan gwamnatin Donald Trump ta mara wa mataimakiyarsa, Delcy Rodríguez, baya a matsayin shugabar ƙasar, inda daga bisani aka rantsar da ita a matsayin shugabar riƙo, sannan ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar man fetur da Amurka.

  4. 'Yan sanda sun ce 'yan bindiga sun kashe mutane 10 a Taraba

    Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari ƙauye Binarri da ke karamar hukumar Karim Lamido, inda suka kashe aƙalla mutum 10, suka yi awon gaba da kayayyakin abinci daga shaguna tare da ƙona gidaje masu yawa.

    Cikin hirarsa da BBC kakakin 'yan sandan jihar Victor Mshelizah ya tabbatar cewa mutum 10 da aka gano gawarsu akwai harbin bindiga a jikinsu.

    "Duka da harbin bindiga jikinsu. Mun gano takwas daga cikin gawarwakin, 6 maza ne, biyu mata ne, kuma mun miƙa wasu ga 'yan uwarsu domin yi musu jana'iza,".

    Jami'in ya ce sun ƙara gano gawarwakin wasu mutane 15 da suka nutse a kogi bayan kifewar kwalekwalensu.

    "Har yazuwa yanzu ba mu kai ga gano su wane ne ba, sannan kuma ba mu gano musabbabin tafiyar da suka yi cikin daren ba, amma dai sun fito ne daga yankin Binnari na Karim Lamido," in ji kakakin 'yan sandan.

    Mshelizah ya ce ya zuwa yanzu sun girke ƙarin jami'ai a yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin mutane.

  5. Za mu fallasa masu yi mana maƙarƙashiya a tafiyarmu - Pantami

    Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bukaci magoya bayansa da su ci gaba da dagewa da addu’o’i tare da kauce wa masu sukarsa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za a fallasa masu yi masa maƙarƙashiya game da burinsa na siyasa.

    Pantami, wanda malamin addinin Musulunci ne, ya mamaye kafafen yaɗa labarai tun bayan da ya bayyana a hukumance aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Gombe.

    Cikin wani bidiyo ya ya wallafa a shafinsa na kafafen sada zumunta, Pantami ya ce da gaske ne duk zargin da ake yi cewa wasu suna yi wa tafiyarsa zagon kasa, "babu kudin da ba a bayarwa domin kassara tafiyar nan".

    Kuma a kusa za su bayyana sunayen mutanen da "suke mana munafirci" kuma ba a ganin bayan wadanda suke yin tafiya domin Allah.

    A baya ya kasance mamba a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), amma ya fice daga jam’iyyar bayan ta amince da Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin ɗan takararta a zaɓen gwamna na jihar.

    Daga bisani ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin ci gaba da neman cikar burinsa na siyasa, inda ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a ranar 26 ga Mayu, 2026.

    Sai dai ɗaya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan PDP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya kalubalanci nasarar Pantami a Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe. Kotun ta soke zaɓen fidda gwani tare da umartar a sake gudanar da wani, wanda Pantami ya sake lashewa.

    Amma hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar 24 ga Satumba wanda ya hana jam’iyyun siyasa tsayar da ‘yan takarar da sunayensu ba su cikin kundin rajistar mambobin jam’iyya da aka miƙa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a cikin wa’adin da doka ta tanada, ya haifar da rashin tabbas kan yiwuwar Pantami ya shiga zaɓen shekarar 2027.

    Ko da yake INEC ta sanya sunansa cikin jerin ‘yan takarar gwamna da ta fitar a ranar 29 ga Agusta, sabon jerin sunayen da hukumar ta fitar a watan Oktoba bai ƙunshi sunan Pantami ba.

    Ya tabbatar wa magoya bayansa cewa za a warware matsalar, yana mai bayyana cire sunansa daga jerin a matsayin wani ƙalubale na wucin gadi da ba sabon abu ba ne a cikin tsarin zaɓe

  6. 'Iran ta sake buɗe mashigar Rimdan ta tsakaninta da Pakistan'

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito sake buɗe mashigar iyakar Rimdan tsakanin Pakistan da Iran

    Peyman Sanandji, shugaban Kwamitin Sufuri na na Tehran, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Mehr cewa an dawo da harkokin kasuwanci a mashigar iyakar Rimdan tsakanin Iran da Pakistan.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars ma ya ruwaito cewa Pakistan ta sake buɗe mashigar iyakar Gabd-Rimdan da ke yankin Gwadar, inda jigilar manyan motoci masu ɗauke da iskar gas an LPG da sauran kayayyakin masarufi ta koma kamar yadda aka saba.

    Fars ta ce Pakistan ta rufe mashigar a cikin makon da ya gabata ne saboda dalilan tsaro da kuma yaƙi da safarar kayayyaki ba bisa ƙa'ida ba.

    A wani ɓangare na tattaunawarsa da kamfanin Mehr, Peyman Sanandji ya ce dangane da mashigogin kan iyaka tsakanin Iran da Iraki, dukkan mashigogin suna aiki yadda ya kamata ban da mashigar Al-Shayb, kuma zirga-zirga na gudana ba tare da wata matsala ba.

    Ana sa ido sosai kan labaran da suka shafi ayyukan mashigogin ƙasa tsakanin Iran da maƙwabtan ƙasashenta bayan da Amurka ta sanar da fara wani shiri na takaita harkokin tattalin arzikin Iran.

  7. Saudiyya ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami na Yemen

    Ƙawancen sojin Saudiyya ya ce ya kakkaɓo makamai masu linzami 10 da aka harba daga Yemen

    Ƙawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta wajen yaƙi da mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran a Yemen ya ce ya kakkabo makamai masu linzami 10 da aka harba zuwa kudancin Saudiyya.

    Hukumomin ƙasar sun kuma ce sun kakkabo wani makami mai linzami da aka harba domin kai hari kan babban birnin ƙasar, Riyadh.

    A yau Lahadi ne ake sa ran Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sarki Khalid da ke Riyadh zai koma aiki bayan an rufe shi makonni biyu da suka gabata sakamakon munanan hare-haren makamai masu linzami da suka yi sanadiyar asarar rayuka.

    Har yanzu ba a bayyana cikakken matsayin yadda zirga-zirgar jiragen sama ke gudana a filin jirgin saman ba, amma mayaƙan Houthi sun yi gargadin cewa filin jirgin saman na ci gaba da kasancewa cikin wuraren da suke iya kai wa hari.

    Houthi dai sun sha kai hare-hare kan filin jirgin saman tun bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da Saudiyya da ƙawayenta ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan da ƙungiyar ke iko da su a Yemen.

  8. Sojojin Iran sun kai hari a Iraq

    Rahotanni sun ce dakarun IRGC sun kai hari da jirgin sama maras matuƙi kan sansanin Komala a Yankin Kurdistan na Iraki

    Kafafen yaɗa labarai na cikin gida a Iran sun ruwaito cewa Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun kai hari da jirgin sama maras matuƙi kan sansanonin wata jam'iyyar Kurdawa mai adawa da gwamnatin Iran a Yankin Kurdistan na Iraki.

    A cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Mehr, dakarun IRGC sun kai harin ne kan wani sansanin ƙungiyar Komala da ke yankin Balisan a daren jiya, a wani mataki da suka bayyana a matsayin "ayyukan rigakafi kafin afkuwar barazana."

    Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun ce hare-haren sun yi wa ƙarfin sojan ƙungiyar mummunar illa.

    Jam'iyyar Komala Zhudakshan ta sanar a ranar Asabar, 2 ga Nuwamba, cewa ɗaya daga cikin sansanoninta da ke kusa da iyakar Iran da Yankin Kurdistan na Iraki ya fuskanci harin jirgin sama maras matuƙi.

    Jami'in hulɗa da jama'a na Komala, Ali Ranjbari, ya ce harin ya faru ne kusan ƙarfe 10:00 na dare, inda jirgin ya shiga yankin ta mashigar iyaka ta Haji Omran.

    Yankin Kurdistan na Iraki na karɓar sansanoni da cibiyoyin jam'iyyun Kurdawan Iran, waɗanda aka ce an kwace makamansu.

  9. Ba za a samu maslaha ba sai an dakatar da kai hare-hare - Iran

    A cikin sabbin kalamansa, Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi gargaɗi kan rahotannin da ke nuna yiwuwar Amurka da Isra'ila su sake kai wani hari, yana mai cewa: "Za a iya samun tsagaita wuta ne kawai idan an dakatar da gaba ɗaya duk wani rikici a dukkan fannoni."

    Abbas Araghchi ya bayyana haka ne a wajen bikin buɗe "Cibiyar Takardu da Gidan Tarihi na Kamal Kharrazi", inda ya ce an tattauna wannan batu da Amurka a duk tattaunawar da aka gudanar ta hanyar sasancin Pakistan da Qatar.

    Ya ce Kamal Kharrazi, tsohon ministan harkokin wajen Iran kuma mai bai wa tsohon jagoran ƙasar shawara kan harkokin ƙasa da ƙasa, ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a harin da Amurka ta kai.

    A wani ɓangare na jawabinsa, Mista Araghchi ya yi gargaɗi game da abin da ya kira "raɗe-raɗin masu kira ga yaƙi", yana mai cewa Iran za ta ɗora musu nauyi mai tsanani.

    Ya ƙara da cewa: "Makaman rokan Iran sun lalata jiragen yaƙin Amurka da dama yayin da suke a ƙasa."

    Wadannan kalamai na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da Donald Trump ya sake magana kan yiwuwar ɗaukar sabon matakin soja a kan Iran, inda ya ce: "Wataƙila sai na kammala aikin, ko kuma wataƙila su amince da yarjejeniya."

    Ya kuma ce har yanzu bai tabbatar da wace hanya za a bi ba.

    A wani ɓangare na jawabinsa, Araghchi ya ce: "Hanyoyin zirga-zirga a mashigar Hormuz ba za su kasance kamar da ba. Tsarin gudanar da mashigin Hormuz ma ba zai kasance kamar da ba. Waɗannan batutuwa ne da aka tattauna tsakaninmu a yayin tattaunawa, kuma za a ci gaba da tattauna su."

  10. An fara kaɗa ƙuri'a zaɓen shugaban ƙasar Brazil

    An gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe na ƙarshe a ƙasar Brazil, gabanin zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a ranar Lahadi.

    Shugaban ƙasar mai ci, Lula da Silva, ya shaida wa ɗimbin magoya bayansa a birnin Sao Paulo cewa har yanzu suna da damar sauya alƙiblar zaɓen, bayan da ya sha kaye a zagayen farko.

    A nasa ɓangaren, abokin hamayyarsa na jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi, Flavio Bolsonaro, ya halarci wani jerin gwanon mashin a jihar Minas Gerais, wadda ake kallon muhimmiyar jiha ce wajen tantance sakamakon zaɓen.

    Wakiliyar BBC ta ce ana kallon cewa ɗan takarar shugaban ƙasar Flávio Bolsonaro ne ke da damar lashe zaɓen bayan da ya zo na farko a zagayen farko na kaɗa ƙuri'a da aka gudanar a farkon wannan watan.

  11. Duk ƙasar da ta taɓa mu, za mu mayar da martani - Iran

    Mohammad Bagher Qalibaf, a martani ga barazanar da manyan jami'an Amurka suka yi kan yiwuwar sake kai wa Iran hari ta soja, ya ce: "Za mu mayar da martani ga wanda zai bayar da mamaki ga duk wani yunƙurin na keta hurumin ƙasar Iran."

    Kakakin Majalisar Dokokin Iran kuma babban mai tattaunawar ƙasar ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar kafin fara zaman majalisar a ranar Lahadi.

    A wannan zama, ƴan majalisar sun ci gaba da nazarin wani kudiri da ake kira "Tsarin Tunkarar Tasirin Waje".

    Kashi biyu bisa uku na ƴan majalisar ne suka halarci zaman na yau, wanda aka gudanar ta hanyar haɗaka, inda wasu suka halarta kai tsaye a zauren majalisar, yayin da wasu suka shiga ta yanar gizo.

    Mista Qalibaf na daga cikin waɗanda suka isa ginin majalisar domin halartar zaman kai tsaye.

    Majalisar Dokokin Iran ta shafe watanni tana gudanar da zamanta ne ta hanyar yanar gizo.

  12. Gabon ta ɗage haramcin amfani da kafafen sadarwa

    Gabon ta ɗage haramcin amfani da kafafen sada zumunta bayan wata takwas da hukumar kula da harkokin yaɗa labarai ta ƙasar ce ta rufe kafafan sada zumunta da suka hada da Facebook, da TikTok, da YouTube da kuma Instagram.

    Hukumar ta ɗauki matakin a lokacin tana mai zargin cewa wasu abubuwan da ake wallafawa a cikinsu na haddasa rikici da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'umma.

    An sanya dokar ce a lokacin da shugaban kasar, Brice Oligui Nguema, ke fuskantar zanga-zanga da tashe-tashen hankula ƙasa da shekara guda bayan zaɓensa.

    Sai dai jam'iyyun adawa sun yi Allah-wadai da matakin, suna masu cewa amfani da irin wannan iko tamkar amfani da mulki ne fiye da kima.

  13. An kama aƙalla masu zaga-zangar tsadar rayuwa 1,000 a Faransa

    Mahukunta a ƙasar Faransa sun ce sun kama kusan mutum dubu guda a yayin wata zanga-zangar gama-gari da aka gudanar a faɗin ƙasar domin nuna adawa da tsadar rayuwa.

    An samu rikici a birnin Paris da wasu birane bayan dubban daruruwan mutane sun fito kan tituna, inda 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye, yayin da wasu masu zanga-zangar suka rika jefa abubuwan wasan wuta da makamantansu.

    Sai dai hukumomi sun ce rikicin bai kai girman tarzomar da ta mamaye sassan kasar a irin wannan zanga-zangar da aka gudanar a karshen makon jiya ba.

    Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Laurent Nuñez, ya ce jami'an tsaro sun fuskanci munanan hare-hare daga masu ra'ayin kawo sauyi.

  14. Dubban Isra'ilawa sun yi zanga-zangar adawa da Netanyahu

    Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Tel Aviv a ranar Asabar, 24 ga Oktoba, kwanaki uku kafin gudanar da zaɓen majalisar dokokin Isra'ila.

    Zaɓen na zuwa ne a lokacin da yaƙin Gaza da aka kwashe shekara uku ana yi, da kuma arangama ta soji da Lebanon da Iran, tare da damuwa kan yadda Isra'ila ke ƙara fuskantar keɓewa a idon duniya da kuma tasirin hakan ga tattalin arzikinta, suka zama manyan batutuwan da ke tasiri a siyasar ƙasar.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce shugabannin manyan jam’iyyun adawa huɗu, ciki har da Gadi Eisenkot, tsohon hafsan hafsoshin rundunar sojin Isra'ila kuma babban abokin hamayyar siyasa na Firaiminista Benjamin Netanyahu, sun halarci gangamin na ranar Asabar.

    Ƙungiyar da ake kira “October Council”, wadda iyalan waɗanda aka kashe da kuma waɗanda aka yi garkuwa da su a harin Hamas na ranar 7 ga Oktoban 2023 suka kafa, ce ta shirya zanga-zangar.

    Ƙungiyar na kira da a kafa wani kwamiti mai zaman kansa na gwamnati domin binciken gazawar tsaro da ta ba da damar kai harin na Hamas, tare da tantance irin alhakin da jami’an Isra'ila suka ɗauka kan lamarin.

  15. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi, inda za mu cigaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta