Najeriya ta amince da kashe dala miliyan 45 kan ƙarfafa matakan kariya a filayen jiragen sama
Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe dala miliyan 45.8 domin kafa tsarin kare lafiyar jama'a da kuma tunkarar barazana yaɗuwar cutuka a manyan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa guda biyar na Najeriya, domin ƙarfafa ƙarfin ƙasar wajen gano da kuma dakile yaɗuwar cututtuka masu yaɗuwa.
Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, kamar yadda gidan talibijin na Channels ta ruwaito.
Ya ce an shafe shekara biyu ana shirya wannan aiki, kuma za a aiwatar da shi ne ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu na tsawon shekara 20.
A cewar Pate, an tsara wannan shiri ne domin cike giɓin da ke akwai a fannin lafiyar jama'a a kan iyakokin Najeriya, waɗanda sama da fasinjoji miliyan 18 ke bi ta cikinsu duk shekara.
Shirin zai shafi Filin Jiragen Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas, Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, Mallam Aminu Kano da ke Kano, Akanu Ibiam da ke Enugu, da kuma Filin Jiragen Sama na Port Harcourt da ke Omagwa.
Ya ce Najeriya ta daɗe tana sanya ido sosai a ƙofofin shigowa ƙasar tun kafin tabbatar da ɓullar Ebola a ranar 19 ga Oktoba.
Ya ƙara da cewa mara lafiyar da aka gano da cutar ta samu sauƙi, yayin da ake ci gaba da bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da ita.