Brentford ta kammala daukar mai tsaron bayan West Ham, El Hadji Malick Diouf, a yarjejeniya da darajarta za ta iya kaiwa fam miliyan 40.
Dan wasan bayan hagu dan kasar Senegal mai shekaru 21 ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar, tare da zabin kara masa shekara guda.
A karkashin yarjejeniyar, Brentford za ta biya fam miliyan 35 a farko, sannan karin fam miliyan 5 ta hanyar wasu sharuddan kari.
Diouf ya buga wasan farko na West Ham a Championship da Burnley, amma ba a saka shi cikin tawagar wasanni biyu na gaba ba yayin da ake ci gaba da tattaunawar cinikinsa.
Shi ne babban dan wasan baya da Brentford ta fi mayar da hankali wajen nema a wannan kasuwar musayar 'yan wasa. Tattaunawar ta tsaya cak a farkon bazarar nan kafin a sake farfado da ita a farkon wannan makon.
Diouf ya dawo Premier League bayan West Ham ta fadi daga gasar a kakar da ta gabata.
Haka kuma, sayar da shi ya kawo wa West Ham riba mai yawa, domin sun saye shi daga Slavia Prague kan fam miliyan 19 ne shekara guda da ta wuce.
Diouf ya buga wasanni 34 a West Ham a kakar da ta gabata, inda ya taimaka aka zura kwallaye biyar.
Kocin Brentford, Keith Andrews, ya ce "Shi dan wasa ne da ya dace da tsarin shekarun da muke nema, kuma har yanzu yana da babban damar ci gaba da inganta kansa."
Diouf kuma ya ce Andrews ya gamsar da shi cewa zai iya ci gaba da bunƙasa da inganta wasansa a Brentford.