Sabon kocin tawagar Faransa, Zinedine Zidane, ya sanar da jerin ƴan wasan da ya gayyata a karon farko ranar Juma’a, domin wasannin Nations League masu zuwa, inda ya haɗa da wasu sabbin fuskoki ciki har da mai tsaron bayan Liverpool, Jeremy Jacquet, wanda ke taka rawar gani a kakarsa ta farko a Anfield.
Zidane, mai shekara 54, wanda ƙwarewarsa ta taimaka wa Faransa lashe Kofin Duniya na farko a tarihinta a matakin dan wasa a shekarar 1998, ya koma jagorancin tawagar da nufin mayar da Faransa kan ganiya.
Zidane ya samu babbar nasara a aikin horarwa a tsohuwar ƙungiyarsa ta Real Madrid, inda ya jagoranci ƙungiyar Spaniya zuwa lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere.
Ana sa ran irin wannan nasara daga gare shi a Faransa, wadda ke da wasu daga cikin ƙwararrun ƴan wasan ƙwallon ƙafa a duniya, yayin da take shirin gasar Euro 2028 da Kofin Duniya a 2030.
Faransa ta lashe Kofin Duniya a shekarar 2018, ta zama ta biyu a gasar bayan Argentina a shekarar 2022, sannan ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar bana.
Mai tsaron raga Guillaume Restes da ƴan wasan da ke tsaron bayan, Jacquet da Andy Diouf da ɗan wasan tsakiya, Lucas Da Cunha da ɗan wasan gaba Esteban Lepaul na daga cikin ƴan wasan da Zidane ya fara gayyata zuwa babban tawagar ƙasar a karon farko.
Ɗan wasan Real Madrid, Aurelien Tchouameni na daga cikin fitattun ƴan wasan da ba a baiwa goron gayyata.
An naɗa Zidane a matsayin kocin Faransa kan yarjejeniyar zuwa Kofin Duniya na 2030 a watan Yuli, inda ya maye gurbin Didier Deschamps. Hakan ya sanya shi zama mutum na uku daga cikin tawagar Faransa da ta lashe Kofin Duniya na 1998 da ya jagoranci Les Bleus.
Zidane zai fara jagorantar Faransa a karon farko a wasan matakin rukuni a Nations League da za ta kara da Turkiyya a Izmit ranar 25 ga watan Satumba.
Daga nan Faransa za ta ziyarci Belgium, kafin ta karɓi bakuncin Italiya da Belgium a watan Oktoba.
Masu tsaron raga: Mike Maignan (AC Milan), Guillaume Restes (Toulouse), Robin Risser (Lens)
Ƴan baya: Andy Diouf (Inter Milan), Jeremy Jacquet (Liverpool), Pierre Kalulu (Juventus), Ibrahima Konate (Real Madrid), Jules Kounde (Barcelona), Maxence Lacroix (Chelsea), Adrien Truffert (Bournemouth), Dayot Upamecano (Bayern Munich)
Ƴan wasan tsakiya: Eduardo Camavinga (Real Madrid), Rayan Cherki (Manchester City), Lucas Da Cunha (Como), Manu Kone (AS Roma), Adrien Rabiot (AC Milan), Warren Zaire-Emery (Paris St-Germain)
Ƴan wasan gaba: Bradley Barcola (Liverpool), Ousmane Dembele (PSG), Desire Doue (Paris St-Germain), Esteban Lepaul (Rennes), Kylian Mbappe (Real Madrid), Michael Olise (Bayern Munich)