Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ibrahim Traoré: Me ya sa Burkina Faso ta haramta amfani da kalmomin "matalauciyar ƙasa" da "ƙaramar ƙasa"?
Firaminista Rimtalba Jean Emmanuel Ouédraogo da Shugaba Ibrahim Traoré suna riƙe da littafi yayin baje kolin ayyukan gwamnati da aka gudanar a farkon watan Oktoban 2026.
Tun bayan fara sabon zangon karatu a ranar 1 ga Oktoban 2026, hukumomin Burkina Faso suka fara wani tsari na "kawar da tasirin mulkin mallaka" daga tarihin da ake koyarwa a tsarin iliminsu.
A Burkina Faso, gwagwarmayar adawa da daular mulkin mallaka da hukumomi ke fafutawa tun bayan ayyana Juyin Juya Halin Jama'a na Ci Gaba a watan Afrilun 2025 karkashin Kyaftin Ibrahim Traoré, tana kuma haɗa da juyin juya hali a fannin tunawa da tarihi, kamar yadda hukumomin suka bayyana.
A cikin wata sanarwa ranar 7 ga Satumban 2026, Ministan Ilimin Sakandare da Horar da Sana'o'i da Fasaha, Farfesa Moumouni Zoungrana, ya ce akwai "kalmomi a darussan tarihi da ilimin ƙasa da ba sa girmama mu."
Ya ce: "Wannan na nufin cewa a cikin littattafanmu ma akwai ƙaryoyi da aka rubuta domin a raina mu, a ƙasƙantar da mu, a hana mu tunani yadda ya kamata. Kuma mun shafe lokaci muna inganta waɗannan munanan dabi'u da muka ci gaba da gadarwa daga tsara zuwa tsara."
Ya ƙara kira ga al'ummar ilimi na Burkina Faso da su nuna "jarumtar rushe komai baki ɗaya tare da juya teburin gaba ɗaya."
Daga nan Farfesa Zoungrana ya sanar da sake duba manhajojin karatu, ciki har da Tarihi, Ilimin Ƙasa da Ilimin Ɗan Ƙasa, domin cire kalmomin da ya bayyana a matsayin "waɗanda ba su dace ba."
Ana kallon waɗannan fannoni uku a matsayin mafiya gaggawa, yayin da ƙasar ke shirin babban garambawul na tsarin ilimin Burkina Faso mai suna "Neekre Pact" (wato farkawa a Faransanci) wanda aka ƙaddamar ranar 17 ga Oktoba.
Yayin da ake jiran a sake rubuta littattafan Tarihi, Ilimin Ƙasa da Ilimin Ɗan Ƙasa gaba ɗaya, an riga an raba wa malamai wata takarda mai ɗauke da sauye-sauyen gaggawa.
Sauye-sauyen sun haɗa da maye gurbin wasu kalmomi, ƙara sababbin darussa da kuma haramta wasu kalmomi da wasu darussa.
Ga wasu kalmomi da darussa da suka sauya a Burkina Faso tun daga ranar 1 ga Oktoba:
1. Kalmomin da suka sauya
A darasin Tarihi, kalmomi da jimloli 27 sun daina kasancewa cikin ƙamus ɗin malamai da ɗalibai.
Mamaya da 'yan leƙen asiri
Daga cikin sauye-sauyen da aka yi, kalmar mulkin mallaka yanzu ta zama mamayar daular mulkin mallaka, mai mulkin mallaka ko ɗan mulkin mallaka ya zama mamayi, yayin da masu bincike suka koma 'yan leƙen asiri, sannan yankunan mallaka suka zama yankunan da aka mamaye.
Yanzu ana amfani da kalmar mamayar daular Faransa a Burkina Faso wajen bayyana mulkin mallakar Faransa a Burkina Faso.
'Yantar da Afirka
Yanzu ana kiran kawar da mulkin mallaka da samun 'yancin kai da sunan 'Yantar da Afirka.
Hakazalika, an rarraba lokaci gida biyu: kafin mamaya da bayan mamaya, maimakon zamanin kafin mulkin mallaka da bayan mulkin mallaka.
Yaƙin sake mamaya
Daga yanzu, ta'addanci ana bayyana shi da sunan yaƙin sake mamaya.
Kalmar "sojojin Senegal" ta koma "mayaƙan yaƙin Afirka", yayin da "tsofaffin mayaƙa" suka koma "tsofaffin mayaƙan yaƙin Afirka".
Darussan tarihi kamar cinikin bayi ta gabas da kuma cinikin bayi yanzu ana kiransu korar 'yan Afirka ta Gabas da kuma ta Tekun Atlantika.
A ilimin ƙasa kuma, kusan kalmomi goma da aka ɗauka a matsayin "marasa mutunci" sun daina amfani.
Burkina Faso, wadda ake bayyana a matsayin ƙasa da ba ta da hanyar fita zuwa teku, yanzu ana kiranta ƙasa ta nahiyar ciki; kalmar ƙabilu ta koma ƙungiyoyin zamantakewa da al'adu; yayin da rauni da ƙuntatawar ƙasar yanzu suke zama ƙalubale da damammaki.
An kuma daidaita ma'anar ci gaba da yanayin ƙasar, inda ta koma ci gaba daga cikin gida.
Darasin Ilimin Ɗan Ƙasa da Tarbiyya (ECM) ya sauya sunansa gaba ɗaya zuwa Ilimin Ɗan Ƙasa da Kishin Ƙasa (ECP).
2. Kalmomi da darussan da suka ɓace
An haramta amfani da wasu kalmomi masu bayyana yanayi kai tsaye, musamman a ilimin ƙasa.
Kalmomi kamar ƙasa matalauciya, ƙasa mai bashi, ƙaramar ƙasa, yanayi mara kyau da sauransu, yanzu an hana amfani da su.
Haka kuma an haramta bayyana ƙungiyoyin zamantakewa da al'adu a kaso na ƙabilu ko kuma a kaso na addinai.
An kuma cire wasu darussa na ilimin ƙasa, musamman waɗanda ake koyarwa a aji na takwas.
Daya daga cikin waɗanda aka cire shi ne darasin "cinikin bayi ta hanyar kasuwancin kusurwa uku".
Wani malami da BBC Africa ta tattauna da shi ya ce an kuma "cire gaba ɗaya babin da ya shafi nazarin ilimin ƙasa na zahiri na Turai."
Ya ce: "An fi mayar da hankali kan yanayin ƙasa da ci gaban Afirka."
3. Sababbin darussa
A lokaci guda kuma, ana ƙara sababbin darussan Tarihi da Ilimin Ƙasa a matakan sakandaren ƙasa da sakandare.
A aji na shida, an ƙaddamar da wani sabon darasi mai taken "Ma'anar Juyin Juya Hali".
Wannan batu ne da hukumomi ke fatan zai zama ginshiƙi wajen kawo manyan sauye-sauye.
Da yake jawabi ga matasan Burkina Faso a bikin Ranar Matasa ta Duniya a watan Agustan da ya gabata, Minista Moumouni Zoungrana ya bayyana cewa "juyin juya hali ne kaɗai zaɓi mai yiwuwa domin samar da katsewa da abin da ya gabata (...) da kuma tabbatar da cikakkiyar 'yancin kai ta fuskar tattalin arziki, kuɗi da siyasa ga Burkina Faso."
An kuma ƙara sabbin darussa biyu a manhajar Tarihi ta aji na biyar.
Su ne "Ilimi da Fasahohin Afirka" da kuma "Juyin Juya Halin Burkina Faso".
Na biyun yana nazartar manufofin Juyin Juya Halin Dimokuraɗiyya da Jama'a (RDP) na Kyaftin Thomas Sankara, wanda ya jagoranci ƙasar tsakanin 1983 da 1987, da kuma Juyin Juya Halin Jama'a na Ci Gaba (RPP) na Kyaftin Ibrahim Traoré, wanda ke gudana tun ƙarshen shekarar 2022.
Ga takwarorinsu da suka fi girma a aji na takwas kuma, an ƙara sabon darasi mai taken "Juyin Juya Halin Haiti".
Darasin yana sake duba ƙungiyoyin da suka yi gwagwarmayar 'yantar da al'ummar Haiti, nasarorinsu da kuma kurakuransu.
A hirarsa ta baya-bayan nan da manema labarai wadda aka watsa a ƙarshen watan Satumba, Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traoré ya yi kira ga 'yan ƙasarsa da su "karanta tarihin Haiti su fahimci cewa bai kamata ku yi wasa da waɗannan mutane ba," yana nufin tsoffin ƙasashen mulkin mallaka.