Jami'an Najeriya sun ceto 'yan hidimar ƙasar da aka yi garkuwa da su
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce jami’an tsaro sun ceto matasan nan 15 da ke aikin yi wa ƙasa hidima, waɗanda aka sace a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima ta Ƙasa (NYSC) ta ce mutanen na daga cikin mutane 21 da aka ceto daga wani daji a Ƙaramar Hukumar Ofu a ranar Litinin, a cewar hukumomin Najeriya. sun haɗa da maza takwas da mata 13.Matasan da suka kammala karatun jami’a sun taso ne daga sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima na NYSC da ke makwabciyar jihar Bayelsa zuwa Abuja, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka tare motocinsu kwanaki da suka gabata.Shugaba Bola Tinubu ya ce an samu nasarar ceton mutanen ne sakamakon wani samame da sojoji, ‘yan sanda, hukumomin leƙen asiri da kuma ‘yan sa-kai na yankin suka gudanar tare.Ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bin sawun waɗanda suka aikata satar domin gurfanar da su a gaban shari’a.