Harin Rasha kan ma’ajiyar makamai kusa da Kyiv ya hallaka mutum 37

Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutum 37 ne suka mutu yayin da kusan 400 suka tsere daga gidajensu bayan wani harin jirage marasa matuƙa na Rasha ya afkawa wata ma’ajiyar makamai ta sojojin Ukraine a wajen birnin Kyiv.
Harin, wanda ya faru a daren Juma’a, ya haddasa fashewar harsasai, nakiyoyi da jiragen yaƙi marasa matuƙa da aka adana a wurin.
Fashewar ta lalata gidaje kusan 130 da ke kusa, ciki har da cibiyar kula da tsofaffi da masu nakasa. Haka kuma mutum 42 sun jikkata, ciki har da yara huɗu.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce bai kamata a ajiye makamai masu fashewa kusa da gidajen jama’a ba, yana mai bayyana lamarin a matsayin sakaci mai girma.
Ya kuma sanar da fara bincike kan jami’an da suka amince da adana makaman a yankin da mutane ke zaune, yayin da ayyukan ceto ke ci gaba a yankin Bucha da abin ya shafa.





















