Masu ƙyamar baƙi sun ake yin zanga-zanga a Afirka ta Kudu
Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutane 300 ne suka gudanar da zanga-zanga a wajen taron shugabannin ƙasashen Kudancin Afirka (SADC) a birnin Durban na Afirka ta Kudu, suna neman a kori baƙin da ba su da takardun zama a ƙasar.
Jagorar masu zanga-zangar, Jacinta Ngobese-Zuma, ta ce sun zo ne domin sanar da shugabannin SADC cewa su kwashe 'yan ƙasashensu da ke zaune a Afirka ta Kudu ba bisa ƙa'ida ba.
Dubban 'yan ƙasashen waje sun fice daga Afirka ta Kudu a watannin baya sakamakon rikicin ƙyamar baƙi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Makamin Rasha ya fashe kusa da iyakar Moldova da Ukraine
Hukumomin Moldova sun ce wani makami mai linzami ya fashe a kusa da iyakar ƙasar da Ukraine.
Rundunar sojin sama ta Ukraine ta ce ta gano wani makami mai linzami na Rasha da ya bi ta sararin samaniyar yankin Odesa, kafin daga bisani ya ɓace daga na'urorin bin diddiginsa.
Wannan ba shi ne karon farko da makamai suka faɗo a ƙasashen da ke makwabtaka da Ukraine ba.
A baya ma an zargi Rasha da tsoma baki a siyasar Moldova da kuma ƙoƙarin dakile shirinta na shiga Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU).
Rahotanni sun ce ƴan bindiga sun kashe mutum 32 a Sokoto
Asalin hoton, Getty Images
Rahitanni sun ce aƙalla mutum 32 ne ake zargin ƴan bindiga sun kashe a wani hari da suka kai garin Ungushi da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto.
Mazauna yankin sun ce maharan sun ɗauki tsawon lokaci a ƙauyukan da abin ya faru, amma wasu mazauna garin sun kashe ƴan bindiga 13 a yayin musayar wut, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito
Wani mazauni garin ya ce ƴan bindigar sun shiga Ungushi ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana ranar Juma’a, lokacin da mutane ke sallar Juma’a inda suka ajiye babura a gaban masallaci, suka tarwatsa masu ibada, sannan suka shiga cikin garin inda suka kashe mutum biyar.
"Bayan maharan sun tafi, mazauna garin suka fara shirye-shiryen binne waɗanda aka kashe, amma sai ƴan bindigar suka dawo suka kashe wasu mutum biyu," in ji shi.
Ya ce daga nan ne suka fara harbe-harbe daga wurare daban-daban tare da kewaye garin, lamarin da ya tilasta wasu mazauna tserewa zuwa cikin gidaje ko hawa wani tsauni domin tsira.
Ya ce ’yan bindigar sun ci gaba da zama a garin har zuwa misalin ƙarfe 1 na dare, sannan suka tafi, "sannan suka sake dawowa da safe suka ci gaba da kashe wasu mutanen."
Ya ce sai da jami’an tsaro suka isa yankin kafin maharan su bar garin.
Sun ce harin ya shafi wasu ƙauyuka da suka haɗa da Umbutu, Maikurhuna, Gwandi, Girkau da Zugu, inda aka sace dabbobi da wasu kayayyaki.
Sai dai rundunar ’yan sandan jihar Sokoto ta ce ba ta da cikakken bayani kan adadin waɗanda aka kashe.
Mayaƙan Houthi sun ce sun kai wa jiragen ruwan Saudiyya hari a Tekun Maliya
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta ce ta kai hari kan wani jirgin ruwan sojan Saudiyya da wasu jiragen ruwa huɗu da ke masa rakiya a Tekun Maliya.
Kakakin rundunar sojan Houthi, Yahya Saree, ya ce an kai harin ne da makamai masu linzami.
Ƙungiyar ta ce daya daga cikin jiragen sojan na Saudiyya na dakon kaya ne, yayin da sauran huɗun da ke masa rakiya jiragen sintiri ne, kuma an kai harin ne kusa da gabar birnin Mokha na Yemen.
Sai dai Saudiyya ba ta fitar da martani kan ikirarin Houthi ba.
Me ya janyo ambaliya a wasu sassan Abuja?
Asalin hoton, UGC
A ƙarshen makon nan ne wasu sassan Abuja, babban birnin Najeriya, suka fuskanci wata mummunar ambaliya da ta haddasa tsaikon zirga-zirga, lalata kadarori, tare da haifar da damuwa ga mazauna yankunan da abin ya shafa.
Lamarin ya sake jawo hankalin jama'a kan yadda birnin ke fama da matsalar ambaliya duk da kasancewarsa ɗaya daga cikin biranen da aka tsara bisa tanadin hukumomi.
Kodayake ruwan sama mai ƙarfi na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliya, masana da dama na ganin matsalar ta wuce yawan ruwan sama.
Karanta abin da ya janyo ambaliyar daga bakin masana a hira da BBC
Ba ma wata tattaunawa da Amurka - Iran
Rundunar Juyin Juya Halin Iran, IRGC, ta musanta cewa tana da wata tattaunawa da Amurka.
Kakakin rundunar, Hossein Mohebbi, ya mayar da martani ga kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ya tabbatar da rahotannin kafafen yaɗa labarai cewa akwai wata hanya ta ɓoye da suke tattaunawa tsakanin Amurka da IRGC.
Mohebbi ya ce: “Wannan ƙaryar ta Trump mafarki ce kawai da ya kamu da shi sakamakon ruɗu da mafarkai na shan kashi da rashin nasara a yaƙin.”
Birgediya Janar Mohebbi ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Tasnim cewa Trump na amfani da irin waɗannan kalamai ne domin ƙoƙarin daƙile hauhawar farashin mai da makamashi a duniya na ɗan lokaci.
Sai dai ya ce hanya ɗaya tilo da Trump ke da ita ita ce ya amince da shan kaye sannan ya aiwatar da sharuɗɗan da Iran ta gindaya.
Trump ya yi barazanar yi wa Oman ruwan bama-bamai idan ta nemi shiga tsakani a batun Iran
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Oman hare-haren bama-bamai masu tsanani idan ƙasar ta “tsoma baki” ko ta kawo cikas ga Amurka a rikicin da take yi da Iran kan mashigar ruwan Hormuz.
Trump ya yi wannan gargaɗin ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da gidan talabijin na Fox News ranar Litinin.
Barazanar ta zo ne yayin da Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta sanar da cewa ta cimma matsaya da Oman kan hanyar da jiragen ruwa za su bi wajen ratsa mashigar Hormuz.
Oman ma ta bayyana cewa tana nazarin tattaunawar da kyakkyawar niyya.
Wani ɗan jaridar Fox News ya ce Trump ya bayyana cewa Amurka na da hanyar sadarwa kai tsaye da Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran, IRGC.
Sai dai daga baya IRGC ta musanta cewa tana tattaunawa da Amurka.
A gefe guda, jami'an Iran sun ce a ranar Litinin suna dab da kammala wata yarjejeniya da Amurka kan yadda jiragen ruwa za su rika bi ta mashigar Hormuz.
Batun sake buɗe mashigar Hormuz na daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna a cikin yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka.
Shugaban China ya kare matakin da ƙasar ta ɗauka kan zanga-zangar 1989
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar China Xi Jinping ya yaba da yadda jam'iyyar Kwaminisanci mai mulki ta murƙushe zanga-zangar dimokradiyya a dandalin Tiananmen.
Ba kasafai ake ambaton abubuwan da suka faru a shekarar 1989 ba a lokacin jawabin cika shekaru 100 da haihuwar ɗaya daga cikin magabata Jiang Zemin wanda ya jagoranci ƙasar China a farkon bunƙasarta.
Jawabin wannan rana, na iya zama yunƙurin Xi na ƙoƙarin bayyana dangantakar gwamnatinsa da ta Jiang, domin karkatar da hankula daga matsalolin da ake ciki yanzu.
Jiang ya fara samun karbuwa ne ya yin da ake tsakiyar zanga-zangar wadda sojoji suka murkushe ta, a wani lamarin siyasa mafi sarkakiya a China
An fara yunƙurin kare harshen mutanen Bajju na Najeriya a Turai
Asalin hoton, UGC
An ƙaddamar da wata ƙungiya wadda manufarta ita ce kare al'adu da harshen mutanen Bajju da ke zama a Birtaniya da kuma ƙasashen Turai.
Ƙaddamarwar wadda ta faru cikin ƙarshen mako a birnin Landan na Birtaniya ta samu halarcin ƴan ƙabilar wadanda suke zaune a ƙasar ta Birtaniya da kuma wasu daga Najeriya.
Al'ummar Bajju na cikin ƙabilun da ke zaune a kudancin Kaduna da kuma wasu jihohi na arewa ta tsakiyar Najeriya, kuma harshen na fuskantar barazana daga manyan harsuna kamar Hausa da turancin Ingilishi.
Ƙungiyar ta ce ɗaya daga cikin manufofin kafa ta ita ce tabbatar da cewa matasan ƙabilar da ake haifa a ƙasashen Turai sun riƙe al'ada da harshen na Bajju.
Asalin hoton, UGC
Ƙabilu ƴan Afirka da dama na fuskantar ƙalubalen tabbatar da cewa matasan da ake haifa kuma suke tasowa a ƙasashen Turai sun riƙe al'adu da harsunansu na asali.
Firaministan Kurdistan na Iraq ya yi allawadai da harin Iran kan ofishinsa
Asalin hoton, Getty Images
Firaministan yankin Kurdistan na Iraq, Masrour Barzani, ya yi allawadai da abin da ya bayyana a matsayin harin jiragen yaƙi marasa matuƙi na Iran kan ofishinsa da kuma gidan shugaban hukumar leƙen asirin yankin.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Barzani ya ce bayanan da binciken Hukumar Yaki da Ta'addanci ta gwamnatin Kurdistan suka tattara sun tabbatar da cewa Iran ce ta kai harin.
Ya bayyana lamarin a matsayin "aikin da ba za a amince da shi ba" tare da yin tir da shi."
Firaministan ya ce harin wani mataki ne mai haɗari na ƙara tashin hankali, kuma barazana ce kai tsaye ga tsaro da zaman lafiyar yankin.
Tun da farko, Hukumar Yaki da Ta'addanci ta Kurdistan ta ce babu wanda ya mutu ko ya jikkata a harin, tana mai cewa an harba jiragen Hadid 110 guda biyu masu ɗauke da abubuwan fashewa daga wajen iyakar Iran.
An kama wata mata da ake zargi da satar jariri a Kebbi
Asalin hoton, Getty Images
'Yansanda a jihar Kebbi sun ce sun kama wata mata mai shekara 19 a ƙaramar hukumar Zuru bisa zargin satar wani jariri da kuma gabatar da shi ga mijinta a matsayin ɗanta.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne bayan matar ta ziyarci mahaifiyar jaririn jim kaɗan bayan haihuwar yaron, inda ta yi alƙawarin kawo mata ruwan zafi amma ta tsere da jaririn.
Binciken farko ya nuna cewa wadda ake zargin ta yaudari mijinta na tsawon watanni tana mai nuna masa cewa tana da juna biyu.
Daga bisani ta sace jaririn tare da kai shi gida tana cewa nata ne.
'Yansanda sun ce an kama matar ne a ranar 14 ga Agustan 2026 bayan bincike, sannan an ceto jaririn tare da mayar da shi ga mahaifiyarsa.
Rundunar ta ce za a gurfanar da wadda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.
Yadda aka yi bikin nuna al'adu a Jami'ar Ahmadu Bello
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yadda ɗaliban jamiʼar Ahmadu Bello da ke Zariya suka yi bikin baje-kolin alʼadu. Ɗaliban ABU kan shirya wannan taro a duk shekara.
Jarumar fina-finan Amurka Hayden Panettiere ta rasu
Asalin hoton, Getty Images
Fitacciyar jarumar fina-finan Amurka, Hayden Panettiere, wadda ta shahara a shirye-shiryen talabijin na Heroes da Nashville, ta rasu tana da shekara 36 a duniya.
Mahaifinta ya tabbatar da rasuwarta a wata sanarwa, inda ya bayyana ta a matsayin mutum mai kawo farin ciki da ƙauna ga iyalanta da kuma miliyoyin masu kallonta.
An haifi Panettiere a shekarar 1989, kuma ta fara fitowa a fina-finai tun tana yarinya kafin ta taka rawa a manyan fina-finai da suka hada da Remember The Titans, Ice Princess, Scream 4 da Scream VI.
A watan Mayun bana ta wallafa littafin tarihin rayuwarta mai suna This Is Me: A Reckoning, inda ta yi bayani kan ƙalubalen zama tauraruwar yara da kuma gwagwarmayarta da matsalar shaye-shaye da murmurewarta.
Har zuwa yanzu, ba a bayyana musabbabin rasuwarta ba, sai dai wasu kafafen yada labarai sun ce ana gudanar da bincike kan lamarin.
El-Rufai ya shigar da ICPC ƙara kan hana shi ganin iyalansa
Asalin hoton, Nasir El-Rufai/Facebook
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) sabuwar ƙara ta naira biliyan 10 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan hana shi ganin iyalansa yayin da hukumar ke tsare da shi.
A cikin ƙarar da lauyansa Ubong Akpan ya shigar ranar 13 ga Agustan 2026, El-Rufai ya ce ICPC ta hana matarsa Aichatou Asabe da ɗansa Abba El-Rufai ziyartarsa, lamarin da ya ce ya tauye masa haƙƙinsa na samun kulawa daga iyalansa.
Ya ce hana shi hulɗa da iyalansa ya hana shi samun abinci, magunguna da sauran muhimman abubuwan da iyalansa za su kawo masa yayin da yake tsare, duk ba tare da wani sahihin dalili na doka ko umarnin kotu ba.
El-Rufai na kuma neman kotu ta ayyana cewa an karya masa haƙƙoƙinsa na ɗanadam da ƙundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Haka kuma yana neman diyyar naira biliyan 10 kan abin da ya bayyana a matsayin take haƙƙinsa.
Isra'ila ta kama Falasdinawa tara bayan Yahudawa sun kulle su a gidajensu
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na Wafa ya ce dakarun Isra'ila sun kama Falasdinawa tara na iyali guda bayan sun shafe sa'o'i suna maƙale a gidansu sakamakon wani hari da yahudawa kama wuri zauna suka kai.
Rahoton ya ce maharan sun kewaye gidan Mohammad Sabet Majid Hassoun da ke wajen ƙauyen Beit Imrin, arewa maso yammacin Nablus, na fiye da sa'o'i uku a daren Lahadi.
Daga bisani ne sojojin Isra'ila suka mamaye yankin tare da kama duka mutane tara da ke cikin gidan.
Wannan na zuwa ne yayin da wasu iyalai Falasdinawa uku ke ci gaba da kasancewa cikin gidajensu a ƙauyen Qusra da ke kudancin Nablus, bayan da yahudawan suka yi musu ƙawanya.
Ambaliya ta mamaye wasu sassan Abuja
Asalin hoton, USG
Mamakon ruwan sama da aka yi a Abuja ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja lamarin da ya jefa mazauna yankunan cikin halin ƙunci tare da katse zirga-zirga.
Daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa akwai Wuse 2, musamman titin Adetokunbo Ademola, inda ruwa ya mamaye hanyoyi da muhallai.
Bidiyoyi da suka karaɗe kafafen sada zumunta sun nuna yadda motoci da dama suka nutse a cikin ruwa ko kuma suke yawo sakamakon kwararowar ambaliyar.
Haka kuma an ga direbobi da fasinjoji sun makale a wasu hanyoyi yayin da ruwa ya hana ababen hawa wucewa.
Ambaliyar ta kuma shafi yankunan Gudu, Maitama, Lokogoma da hanyar da ke haɗa Gaduwa da Durumi, inda ruwa ya mamaye gada tare da hana zirga-zirga.
Wasu 'yan kasuwa sun rufe shaguna bayan ruwa ya shiga wuraren kasuwancinsu, yayin da mazauna yankunan suka yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa.
Lamarin ya sake tayar da hankali kan matsalar magudanan ruwa a Abuja, musamman ma bayan hukumomin hasashen yanayi sun yi gargadin yiwuwar aukuwar ambaliya a birnin a bana.
Asalin hoton, USG
Hare-hare kan tankokin mai sun rage zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun nuna cewa zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz ta ragu sosai cikin kwanaki biyun da suka gabata bayan hare-haren da aka kai wa tankokin ɗaukar mai a yankin.
Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da tattaunawar Amurka da Iran kan warware rikicin da ke tsakaninsu ta tsaya cik.
Bayanan kamfanin Kepler sun nuna cewa jiragen ruwa biyar ne kawai suka ratsa mashigar a ranar Asabar, yayin da babu ko jirgi guda da ya ratsa a ranar Lahadi.
Wannan ya bambanta da yadda jiragen ruwa 31 suka ratsa mashigar Hormuz a ranar Asabar da Lahadi na makon da ya gabata.
Gwamnatin Yemen ta ce ta kai hare-hare kan wuraren 'yan Houthi a sassa daban-daban
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Yemen ta sanar da kai hare-haren bindigogi da na jiragen yaƙi marasa matuƙa kan wuraren mayakan Houthi a lardunan Al-Jawf da Marib.
Dakarun gwamnatin, masu samun goyon bayan Saudiyya, sun ce sun kai hare-hare 181 a sassa daban-daban cikin kwanaki biyu, lamarin da suka ce ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mayaƙar da dama.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa Yemen na fuskantar barazanar komawa cikakken yaƙi duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kafa tun 2022.
Matakanmu na kare kai ne zuwa yanzu, amma za su iya komawa hare-hare - Iran
Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin shugaban harkokin siyasa na dakarun juyin juya halin Iran, Yadollah Javani, ya ce matakan da Iran ke ɗauka a yaƙin da ake yi a halin yanzu na kare kai ne, amma za su iya komawa na kai hare-hare a gaba.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin da rediyon ƙasar Iran, Javani ya ce maƙiyan Iran ne suka fara yaƙin, kuma martanin Iran ya kasance na kare kanta.
Iran ta kuma ce za ta ɗauki duk matakin da ya dace domin kare ƙasar da kuma daƙile barazanar maƙiya, tare da yiwuwar sauya salon martaninta idan lamarin ya buƙaci hakan.
Ya ce rundunonin sojin Iran za su ɗauki sabbin matakai bisa umarnin da aka bayar, tare da ɗaukar duk wani mataki da ya dace don kare ƙasar, tabbatar da tsaro da kuma dakile barazanar maƙiya a lokacin da ya dace.
Kalaman Javani na zuwa ne bayan mai bai wa babban kwamandan IRGC shawara, Mohammad Reza Naqdi, ya bayyana cewa Iran ta yanke shawarar sauya aƙidar soja daga ta kare kai zuwa wadda ta haɗa da kai hare-hare idan an ga hakan ya zama dole.
Iran ta saka sharaɗin buɗe mashigar Hormuz
Asalin hoton, IRNA
Mataimakin shugaban harkokin siyasa na dakarun juyin juya halin Iran (IRGC), Yadollah Javani, ya ce Iran ba za ta buɗe mashigar Hormuz ba sai idan Amurka ta cika nauyin da ke kanta ƙarƙashin yarjejeniyar Islamabad.
A wata hira da ya yi da Ƙungiyar Matasan 'Yan Jarida ta Iran, Javani ya ce dole ne yaƙin ya ƙare bisa tanadin yarjejeniyar Islamabad, yana mai ƙara da cewa buɗe mashigar Hormuz zai biyo bayan cika alƙawurran Amurka da ke cikin yarjejeniyar.
Ya kuma ce mashigar Hormuz da tsarin da za a tafiyar da ita ba za su sake komawa yadda suke kafin ɓarkewar yaƙin ba.
Javani ya zargi Amurka da Isra'ila tare da ƙawayensu da ƙoƙarin ƙwace ikon mashigar Hormuz daga hannun Iran tsawon watanni, amma ya ce duk da haka ba su yi nasara ba.
Haka kuma ya ce tattaunawar da ake yi yanzu game da wata hanyar ruwa tsakanin Iran da Oman za ta kasance ne bayan ƙarshen yaƙin, yana mai jaddada cewa babu shakka yaƙin zai zo ƙarshe"