Rahitanni sun ce aƙalla mutum 32 ne ake zargin ƴan bindiga sun kashe a wani hari da suka kai garin Ungushi da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto.
Mazauna yankin sun ce maharan sun ɗauki tsawon lokaci a ƙauyukan da abin ya faru, amma wasu mazauna garin sun kashe ƴan bindiga 13 a yayin musayar wut, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito
Wani mazauni garin ya ce ƴan bindigar sun shiga Ungushi ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana ranar Juma’a, lokacin da mutane ke sallar Juma’a inda suka ajiye babura a gaban masallaci, suka tarwatsa masu ibada, sannan suka shiga cikin garin inda suka kashe mutum biyar.
"Bayan maharan sun tafi, mazauna garin suka fara shirye-shiryen binne waɗanda aka kashe, amma sai ƴan bindigar suka dawo suka kashe wasu mutum biyu," in ji shi.
Ya ce daga nan ne suka fara harbe-harbe daga wurare daban-daban tare da kewaye garin, lamarin da ya tilasta wasu mazauna tserewa zuwa cikin gidaje ko hawa wani tsauni domin tsira.
Ya ce ’yan bindigar sun ci gaba da zama a garin har zuwa misalin ƙarfe 1 na dare, sannan suka tafi, "sannan suka sake dawowa da safe suka ci gaba da kashe wasu mutanen."
Ya ce sai da jami’an tsaro suka isa yankin kafin maharan su bar garin.
Sun ce harin ya shafi wasu ƙauyuka da suka haɗa da Umbutu, Maikurhuna, Gwandi, Girkau da Zugu, inda aka sace dabbobi da wasu kayayyaki.
Sai dai rundunar ’yan sandan jihar Sokoto ta ce ba ta da cikakken bayani kan adadin waɗanda aka kashe.