KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/09/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 01 ga watan Satumbar 2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Diginza

  1. Za mu koma aiwatar da yarjejeniya idan har Amurka ta cika alƙawuranta - Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ƙasarsa za ta koma aiwatar da yarjejeniyar Islamabad nan take idan Amurka ta koma cika alƙawuran da ta ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar.

    Yayin da yake jawabi a taron Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai, Pezeshkian ya ce Iran a shirye take ta mayar da martani iri ɗaya idan Washington ta mutunta yarjejeniyar.

    A wani ɓangaren kuma, rundunar sojin Iran ta sake gargaɗin ƙasashen yankin cewa za ta kai farmaki ga duk wata ƙasa da aka yi amfani da yankinta wajen kai mata hari.

    Rahotanni sun kuma ce an kai hari kan wani tankar ɗanyen mai a mashigar Hormuz, yayin da Sakataren Sojin Amurka Daniel Driscoll ya yi murabus bayan samun saɓani da Sakataren Tsaro Pete Hegseth.

  2. NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

    ...

    Asalin hoton, NAPTIP/X

    Hukumar hana fataucin mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta ce ta ceto yara sama da 180 da aka yi safararsu daga jihohin Kaduna, Anambra, Benue, Nasarawa da wasu wurare a ƙasar.

    Hukumar ta bayyana cewa wasu ƙungiyoyin masu fataucin yara na yaudarar iyaye ta hanyar bayyana kansu a matsayin ma'aikatan ƙungiyoyin farar hula masu tallafa wa yara da ilimi, sannan su tafi da yaran da sunan ba su ilimi da tallafi.

    A baya-bayan nan, an ceto wasu yara uku da aka kwaso daga Kajuru a jihar Kaduna a wani gini da ke Onitsha ta jihar Anambra, yayin da aka kuma gano wani yaro a hannun wata ma'aikaciyar lafiya.

    NAPTIP ta ce wasu daga cikin yaran da aka ceto an kai su gidajen marayu inda aka rika sayar da su ga mutane da sunan ɗaukar yara reno.

    Hukumar ta ce tana ci gaba da farautar masu hannu a wannan laifi domin gurfanar da su a gaban kuliya.

  3. Sojojin Yemen sun kai wa Houthi hari tare da lalata jiragen ruwansu marasa matuƙi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Yemen sun ce sun kai hare-haren jiragen sama marasa matuƙa kan sansanonin mayaƙan Houthi a yankuna da dama, tare da kai farmaki kan maɓoyarsu da ke yankin Baqim a arewacin lardin Saada.

    A lokaci guda kuma, rundunar ruwan Yemen ta sanar da cewa ta lalata kwale-kwale huɗu marasa matuƙa na ƴan Houthi kusa da tsibiran Hanish da Dhaqr da ke Tekun Bahar Maliya.

  4. Duk wanda ke da hannu a harin Amurka kan tsibirin Larak zai ɗanɗana kuɗarsa - Iran

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Iran ta yi gargaɗin cewa duk wata ƙasa ko ɓangaren da ya taimaka wajen kitsa ko ya goyi baya ko ya shiga cikin shirin harin da Amurka ta kai tsibirin Larak zai ɗanɗana kuɗarsa kuma za su ɗauki alhakin sakamakon da zai biyo baya.

    Iran ta ƙara da cewa za su kuma fuskanci martani mai tsanani kan abin da suka aikata.

    A wata wasiƙa da jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya ya aike wa Sakatare Janar na MDD da Kwamitin Sulhu, ƙasar ta yi Allah wadai da harin tare da kira ga Amurka da ta daina abin da ta kira take haƙƙin ƙundin tsarin MDD da kuma matakan da ke barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Fasha da mashigar Hormuz.

    Haka kuma, rundunar sojin Iran ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani kan duk wata ƙasa da aka yi amfani da yankinta wajen kai hare-hare kan Iran.

  5. Assalamu alaikum

    Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na marhaba da ɗumbin masu bibiyar mu a wannan rana ta Talata.

    Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance tare da ku a don haka sai ku ci gaba da kasancewa da mu.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.