'Babu wata ƙungiyar Musulmi da ke shirin kafa hukumar Hisbah a Filato'
Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a Jihar Filato ta musanta rahotannin da ke cewa akwai wata ƙungiyar Musulmi da ke shirin kafa hukumar Hisbah a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
Sakataren ƙungiyar jihar, Dr Salim Musa Umar, ya ce babu wata ƙungiyar Musulmi da ta sanar da irin wannan shiri, yana mai cewa labarin ya samo asali ne daga wasu hotuna da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI aka yaɗa a kafafen sada zumunta.
Ya bayyana cewa ba za a iya kafa Hisbah a hukumance ba sai da dokar Majalisar Dokokin Jihar Filato, kuma babu irin wannan doka da gwamnati ta kafa.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati da masu amfani da shafukan sada zumunta su riƙa tantance bayanai kafin yaawa domin kauce wa tayar da hankula da kuma kare zaman lafiya a jihar.