Ballon d'or 2026: Kane ne gwarzon dan kwallon kafa na duniya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Harry Kane ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2026 a ranar Litinin bayan kakar wasa da ya zazzaga ƙwallaye a kungiyar Bayern Munich da kuma tawagar Ingila, inda aka tabbatar da shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun masu cin ƙwallaye a tarihin wasan tamaula.

Kane shi ne ɗan Ingila na farko da ya lashe wannan babbar kyauta cikin shekara 25, tun bayan da Michael Owen ya lashe ta a shekarar 2001.

Kyaftin din Ingila ya ci ƙwallaye 61 a wasanni 51 da ya buga wa Bayern a dukkan fafatawa, yayin da ƙungiyar ta Jamus ta lashe Bundesliga da na Jamus guda biyu a lokaci guda.

Ya kuma jagoranci Ingila zuwa wasan kusa da na ƙarshe a Gasar Kofin Duniya, inda ya ci ƙwallaye shida - daga karshe Ingila ce ta uku a wasannin da aka yi a Amurka da Kanada da Mexico, bayan doke Faransa.

Dan wasan Bayern Munich mai shekaru 33 ya zama ɗan Ingila na biyar da ya lashe kyautar, bayan Stanley Matthews (1956), Bobby Charlton (1966) da Kevin Keegan da ya yi bajintar sau biyu (1978 da 1979).

Scotland ta taba samun wanda ya yi nasara ta hannun Denis Law (1964), yayin da Northern Ireland ta samu nata ta hannun George Best (1968), su ma daga cikin wadanda suka lashe kyautar daga United Kingdom.

Dan wasan gaba na Real Madrid da Faransa, Kylian Mbappe shi ne ya yi na biyu, yayin da dan wasan Barcelona da Sifaniya, Lamine Yamal ya kammala jerin ukun farko.

Jerin goman farko da suka yi takarar lashe Ballon d'Or:

1: Harry Kane

2: Kylian Mbappé

3: Lamine Yamal

4: Rodri

5: Lionel Messi

6: Khvicha Kvaratskhelia

7: Ousmane Dembélé

8: Erling Haaland

9: Michael Olise

10: Fabián Ruiz

Gerin wadanda suka lashe kyautuka a bikin Ballon d'Or:

Men's Ballon d'Or winner - Harry Kane

Women's Ballon d'Or winner - Alexia Putellas

Men's striker of the year - Harry Kane

Women's striker of the year - Charlyn Corral

Men's club of the year - Paris St-Germain

Women's club of the year - Barcelona

Socrates Award winner - Bukayo Saka

Men's goalkeeper of the year - Unai Simón

Women's goalkeeper of the year - Cata Coll

Men's coach of the year - Luis de la Fuente

Women's coach of the year - Pere Romeu

Women's young talent of the year winner - Vicky López

Men's young talent of the year winner - Lamine Yamal