Me ya sa magoya bayan Man City ke yi wa taken Premier League ihu?

Manchester City fans holding signs reading 'BOO'
Bayanan hoto, Magoya bayan Manchester City sun ɗaga takadda ɗauke da kalmar "BOO" (ihu) a fili, yayin wani wasan Champions League da suka buga da Sevilla a shekarar 2015.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Hayaniyar ihu da tsangwama a lokacin da ake taken Premier League da Champions League kafin a fara wasa yanzu ya zama ruwan dare a filin wasa na Etihad.

Magoya bayan Manchester City suna nuna fushinsu a wasan da suka buga da Ipswich a ranar Asabar da ta gabata, wanda shi ne karon farko da ta yi a gida tun bayan da aka same su da laifin karya dokokin kuɗi na Premier League.

"Ba zan iya tuna wani wasan gida na Premier League ko Champions League da ba a yi wa taken gasar ihu ba," in ji mai riƙe da tikitin kallon kakar wasannin City, Dave Wilson a wata hira da BBC Sport.

Ana ganin wannan rashin jin daɗin da ake nunawa shugabannin gasar tun kafin a fara wasa ya samo asali ne daga watan Fabrairun 2023, lokacin da aka fara sanar da tuhume-tuhume 115 a kan kungiyar kan karya dokoki.

Daga baya a waccan shekarar, an cire wa Everton maki 10, waɗanda daga baya aka rage zuwa shida bayan ɗaukaka ƙara, bayan an same ta da laifin karya dokokin riba da dorewar kuɗi a dokar ta Premier League.

A wasansu na farko bayan hukuncin, magoya bayan Everton sun nuna fushinsu a filin wasa na Goodison Park ta hanyar yi wa taken gasar ihu da ƙarfi tun kan taka leda, tare da daga jajayen kati da kalmar "corrupt" da aka rubuta a ƙarƙashin tambarin Premier League.

Ko da yake magoya bayan City ba su shirya irin wannan gagarumin gangami ba, amma dai suna bayyana fushinsu.

"Magoya bayan City sun shafe shekaru suna yi wa taken Premier League ihu," in ji Wilson. "Wataƙila abin ya fi tsananta a ranar Asabar saboda wannan ne wasan gida na farko tun bayan sanar da hukuncin samun kungiyar da laifi.

"An daɗe babu wata kyakkyawar alaƙa tsakanin City da Premier League. A wasu wasanni ihun da ake yi yana da ƙarfi fiye da a wasu wasannin. Tabbas ba wani abu ne da aka shirya na musamman don wasan Ipswich ba, amma alama ce ta yadda abubuwa da dama suka taru lokaci guda."

Haka kuma ana jin ihu sosai kafin wasan Champions League da City ta buga da AEK Athens a ranar Talata.

Everton fans
Bayanan hoto, Magoya bayan Everton sun ɗaga kati da yawa da aka rubuta kalmar "corrupt" (cin hanci da rashawa) a ƙarƙashin tambarin Premier League, tare da yin ihu yayin da ake taken gasar kafin fara wasa a watan Nuwamban 2023.
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rashin jin daɗin magoya bayan Manchester City ga UEFA ya samo asali tun shekaru masu yawa da suka wuce, sakamakon jerin saɓani da suka taso tsakaninsu da mahukuntan ƙwallon ƙafa na Turai.

A shekarar 2012, Porto ta fuskanci tarar kusan fam 17,000 daga UEFA bayan City ta kai ƙorafin cewa an yi wa ɗan wasanta, Mario Balotelli kalaman wariyar launin fata.

A wannan kakar wasan kuma, an ci tarar Manchester City kusan fam 24,000 saboda jinkirin minti ɗaya wajen dawowa fili domin ci gaba da karawa da Sporting.

A shekarar 2014, UEFA ta ci tarar City fam miliyan 49 tare da rage yawan 'yan wasan da za ta iya sakawa a jerin da za su buga Champions League, bayan an same ta da karya dokokin Financial Fair Play (FFP).

Shekara shida bayan haka, kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya (CAS) ta soke hukuncin dakatar da City na tsawon shekara biyu daga gasar ta zakarun Turai, bayan ta wanke ta daga zargin "ɓoye kuɗin masu hannun jari a matsayin kuɗin tallafi". Tun farko, UEFA ta yanke hukuncin cewa City ta aikata "manyan laifuffuka" na karya dokokin FFP tsakanin 2012 da 2016.

Wilson ya ƙara da cewa: "Magoya bayan City gaba ɗaya suna ganin akwai wani shiri da ake yi a kansu, kamar yadda ake gani wajen yi wa taken UEFA ihu. Akwai jin cewa ana tsangwamarsu, ko hakan gaskiya ne ko ba haka bane.

"Da alama wasu magoya bayan City ba sa son gasar da muke bugawa ne!"

A halin yanzu, City da magoya bayanta na jiran sakamakon ɗaukaka ƙarar da suka shigar da kuma duk wani hukunci da ka iya biyo baya.

A yanzu haka ƙungiyar ce ke jan ragamar teburin gasar bayan ta lashe dukkan wasanni bakwai da ta buga zuwa yanzu, amma za ta fuskanci babban ƙalubale a wasan waje da Aston Villa ranar Asabar.

Nick Clarke, wanda shi ne shugaban riƙo na The Citizens Trust, ƙungiyar magoya bayan Manchester City, ya ce an kafa ƙungiyar ne a farkon wannan shekarar a lokacin da abin da ya kira "wataƙila mafi girman matsalar da ta taɓa fuskantar magoya bayan City a tarihinta tun daga lokacin da aka kafa ta.

Ko da yake wannan "lokaci ne mai wahala", ya ce magoya bayan suna goyon bayan ƙungiyar gaba ɗaya, kuma aikinsa da yake gudanarwa har da tabbatar da cewa ana jin ra'ayoyinsu duk da hayaniyar da ke kewaye da lamarin.

"Yin ihu ga taken gasar a ranar Asabar ya faru ne kawai ba tare da an tsara ba, in ji Clarke. "Amma ayaba ta roba da aka rarraba a wasan Liverpool wani shiri ne da magoya baya suka tsara tare da haɗin gwiwar ƙungiyar, kuma sun yi babban aiki wajen raba su kafin wasan.

"Duk da cewa akwai magoya bayan da ke cikin ruɗani kan abubuwan da suke faruwa da kungiyar, mafi rinjayen magoya bayan City har yanzu suna ganin Premier League ba ta da tsarin da ya dace wajen kula da kanta da kuma yadda ake tafiyar da ita."

Ko mene ne sakamakon ɗaukaka ƙarar zai kasance, akwai yiwuwar magoya bayan City za su ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kafin fara wasanni.