Mene ne harajin man fetur da Tinubu ke son ɓullo da shi?

Asalin hoton, TAIWO OYEDELE/GETTY
Wata sabuwar muhawara ta kunno kai a Najeriya kan zargin cewa gwamnatin ƙasar na shirin ɓullo da wani sabon haraji da ka iya ƙara tasiri ga farashin man fetur a ƙasar.
Muhawarar ta ƙara ɗaukar hankali ne bayan kalaman ministan kuɗin ƙasar, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gwamnatin ƙasar kan sauye-sauyen haraji, Taiwo Oyedele, waɗanda suka jawo ce-ce-ku-ce tsakanin gwamnati da jam'iyyar hamayya ta ADC.
Yayin da wasu ke bayyana cewa gyaran tsarin harajin da gwamnati ke yi zai iya ƙara wa man fetur kuɗi, jami'an gwamnati na cewa akwai rashin fahimta kan abin da ake shirin aiwatarwa, suna masu jaddada cewa manufar ba ita ce ƙara jefa al'umma cikin wahala ba.
To amma mene ne ainihin abin da gwamnatin ke shiryawa? Shin da gaske ne akwai sabon harajin man fetur da ake son ƙaddamarwa, ko kuwa ce-ce-ku-cen siyasa ne suka haddasa wadannan zarge-zarge?
Wannan ita ce tambayar da ke yawo a tsakanin jama'a a halin yanzu, yayin da yanzu haka ƴan kasar ke kokawa kan tsadar man fetur.
Mene ne ainihin abin da Taiwo Oyedele ya ce kan batun?
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise News a Najeriya, Taiwo Oyedele ya ce kusan dukkan ƙasashen duniya suna da nau'o'in haraji da suke ɗorawa a kan man fetur.
"Idan ka duba ƙasashe daban-daban na duniya, tsakanin kashi 20 zuwa 80 cikin 100 na farashin man fetur haraji iri-iri ne ke ƙunshe a cikinsa."
Ministan ya ce wannan mataki zai inganta tattalin arzikin ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ƙara da cewa, a wasu ƙasashen Afirka ma akwai haraji har kusan iri goma da ake ɗorawa a kan man fetur.
''Amma a lokacin da gwamnati ke biyan tallafi a kan man fetur, ya dace a ce kuma za a ɗora masa haraji? Hakan ba shi da ma'ana, domin gwamnati ce za ta ci gaba da ɗaukar nauyin kuɗin." kamar yadda ya bayyana.
Ministan kudin ya kuma ce "wani abu kuma shi ne, idan ka cire tallafin man fetur, ba zai yiwu a nan take ka fara ɗora masa haraji ba, domin hakan ba zai zama daidai ba, kuma zai haifar da ƙalubale masu yawa ga jama'a."
"Idan muka kai lokacin da tattalin arziki ya daidaita, lokacin da kuɗaɗen shiga na mutane suka isa su iya ɗaukar irin wannan nauyi, a lokacin ne waɗannan haraje-harajen za su zo."
Mista Oyedele ya ci gaba da cewa ba wai saboda muna son ƙara haraji ba ne, amma saboda kuɗaɗen da za a samu daga harajin za a yi amfani da su wajen gina hanyoyi.
"Sannan za a yi amfani da su wajen ƙara yawan tanadin man fetur da ƙasar ke da shi, tare da taimakawa wajen rage yiwuwar ƙarin tashin farashin man a gaba."
Me kalaman ministan ke nufi?
Masana tattalin arziki na kallon kalaman nasa a matsayin wani yunƙuri na kawo tarnaƙi ga tattalin arzikin ƙasar.
Dokta Ashekh Maidugu, malami a sashen nazarin tattalin arziki na Jami'ar Base da ke Abuja, babban birnin Najeriya ya ce shi minista wani jigo ne a gwamnati, wanda kalamansa ke wakiltar maganar gwamnati.
Ya kuma ce a halin da Najeriya ke ciki a yanzu haka game da tattalain arzikinta, duk wani yunkuri na ƙara haraji zai zama barazana ga jama'a wadanda yanzu haka ke cikin ga matsi.
''Shi man fetur kusan ka iya cewa shi ne komai na harkokin rayuwar yau da kullum, kama daga masu kananan sana'o'i da manoma da masu motocin sufuri'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa duk wani ƙarin farashin man fetur a karshe zai ƙare ne a kan talakawan ƙasar.
''Kuma wannan a yanayin da muke ciki ba abu ne da zai zame wa ƙasar alkairi ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ci gaba da cewa ko hasashen Bankin Duniya da IMF suka yi game da bun kasar tattalin arzikin kasar ba nan kusa suka ce ba.
'Wannan ba sabon haraji ba ne'
Tun a watan Satumban 2025 ne Taiwo Oyedele, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X cewa wannan ba sabon haraji ba ne gwamnatin Tinubu ta ƙirƙiro.
Ya ce wannan tanadi tuni yana cikin dokar hukumar da ke kula da gyaran tituna ta ƙasar wato FERMA tun daga shekarar 2007, kawai an sake haɗa shi ne cikin sabon dokar haraji ta Najeriya ta 2025.
A cewarsa, wannan ba yana nufin za a fara aiwatar da shi nan take ba, sai dai kawai gwamnati ta ƙara shi cikin sabuwar doka domin tsarin ya kasance a bayyane da kuma haɗe cikin tsari guda.
Da farko dai an tsara fara aiwatar da wannan ƙarin haraji a watan Janairun 2026, amma daga baya Oyedele ya ce ba a kammala tsayar da ranar da za a fara aiwatar da harajin ba tukunna.
Martanin jam'iyyar ADC?
Ita dai Jam'iyyar adawa ta African Democratic Congress wato (ADC) ta yi gargaɗin cewa "gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta sake laftawa 'yan Najeriya wani karin harajin man fetur tare da kara farashinsa zuwa fiye da naira 1,500 idan ta sake lashe zaɓen 2027."
A cikin martanin da ta fitar ta hannun sakataren yaɗa labaran jam'iyyar Bolaji Abdullahi, ADC ta ce "manufar gwamnatin ita ce fara karɓar harajin man fetur idan har ta sake lashe zaɓen 2027."
Ya ƙara da cewa: "Sun riga sun kafa doka da ta tanadi harajin kashi biyar cikin ɗari kan farashin man fetur. Tun a watan Yunin 2025 ne Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar, amma har yanzu ba a fara karɓar kuɗin harajin ba."
"Sun ajiye aiwatar da shi ne saboda zaɓe mai zuwa. Idan suka ci zaɓen, za su fara karɓar harajin kamar yadda suka cire tallafin man fetur bayan sun hau mulki a shekarar 2023.".






























