Liverpool na harin Luka Vuskovic, AC Milan na son Leny Yoro

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool da Real Madrid na cikin manyan ƙungiyoyin da ke son ɗaukar Luka Vuskovic, da ya koma Brighton daga Tottenham a kakar wasanni. (Football Insider)
Chelsea, da Barcelona, da Bayern Munich su ma na zawarcin Vuskovic, inda suke sa ido akansa. (Teamtalk)
Liverpool ba ta da shirin ɗauko ɗan wasan Trent Alexander-Arnold, a dai dai lokacin da dan wasan ke son ganin ya koma wata babbar ƙungiya a Real Madrid. (Football Insider)
Valencia ta shirya amfani da damar ta wajen tsawaita kwantaragin David Otorbi duk da Liverpool da ke harin ɗan wasan idan suka ninka kudin sakin ɗan wasan kan fam miliyan 50. (Tribuna Deportiva - in Spanish)
Newcastle United da Tottenham na ci gaba da tuntuɓa kan Fikayo Tomori, inda AC Milan ke shirye wajen barin dan wasan ya tafi idan ya na son hakan. (Teamtalk)
AC Milan ha son dan wasan Manchester United Leny Yoro, kan fam miliyan 42. (Calciomercato - in Italian)
Roma na son Alejandro Balde, wanda zai iya barin Barcelona idan bai sami ƙarin damar makin buga wasa ba. (Il Messaggero, via Mundo Deportivo)
























