Me ya sa Tinubu ba ya son a fitar da sakamakon binciken da Amurka ta yi a kansa?

Asalin hoton, Presidency/X
Lauyan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin shugaban na ƙalubalantar fitar da wasu takardun gwamnatin Amurka da ake dangantawa da zarge-zargensa da safarar miyagun ƙwayoyi.
A ƴan kwanakin nan ne Shugaba Tinubu ya nemi wata kotu a Amurka ta hana Ma'aikatar Shari'ar Amurka (DOJ) da hukumomin FBI da DEA fitar da wasu takardunsa da ake dangantawa da zargin safarar miyagun ƙwayoyi da aka taɓa yi masa, a cewar lauyoyinsa.
Tinubu ya shigar da ƙorafi ne a wata shari'ar neman bayanai da wani ɗan gwagwarmayar neman gaskiya a Amurka, mai suna Aaron Greenspan, ya buɗe ƙarƙashin dokar 'Yancin Samun Bayanai (FOIA).
Greenspan na neman a ba shi cikakken kundin FBI da sauran bayanan binciken da suka shafi Tinubu, ciki har da wasu bayanan da suka danganci shari'ar ƙwace kusan dala 460,000 a Amurka a shekarar 1993.
Sai dai lauyoyin Tinubu sun ce fitar da waɗannan takardu na iya keta haƙƙinsa na sirri, suna masu cewa ko da an taɓa bayyana wasu bayanai a baya, har yanzu yana da haƙƙin kare bayanan da ba a fitar da su ba.
Tinubu dai ya sha musanta aikata wani laifi da ya shafi zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Me ya sa Tinubu ba ya so a fitar da bayanan?
Lauyan Shugaba Tinubun, Chris Carmichael, ya ce matakin da Tinubu ya ɗauka na da nufin kare haƙƙoƙinsa na shari'a ne, kuma bai kamata a fassara shi a matsayin amincewa da wani laifi ba
A tattaunawarsa da BBC, Carmichael ya ce shugaban ya yi hakan ne bisa shawarar lauyoyinsa a shari'ar da ake yi a Amurka, lokacin da ya nemi a dakatar da Ma'aikatar Shari'a ta Amurka (DOJ) da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Tarayya (FBI) da kuma Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi (DEA) daga fitar da wasu takardu da bayanan da ake cewa suna da alaƙa da lamarin.
Carmichael ya ce: "Kamar yadda kowane mutum da ke cikin tsarin shari'ar Amurka yake da damar amfani da haƙƙoƙinsa ko kuma ya yi watsi da su, haka ma Shugaba Tinubu yana da wannan damar."
Ya ƙara da cewa: "Idan mutum ya zaɓi ya yi watsi da wasu haƙƙoƙinsa na shari'a, to zai rasa su har abada."
Kalaman lauyan na zuwa ne a daidai lokacin da aka sake mayar da hankali kan yunƙurin da wasu mutane da ƙungiyoyi ke yi na neman ganin wasu takardun da suka shafi zarge-zargen da suka daɗe suna bibiyar shugaban Najeriyar.
Shugaba Tinubu dai ya sha musanta alaƙarsa da safarar miyagun ƙwayoyi, yana mai jaddada cewa babu wata kotu a Amurka da ta taɓa same shi da aikata wani laifi.

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
A cewar Carmichael, tawagar lauyoyin shugaban ce ta ba shi shawarar ya ƙalubalanci fitar da takardun domin kare haƙƙoƙinsa a ƙarƙashin tsarin shari'ar Amurka.
Ya ce: "Bisa shawarar lauyoyi, mun ba shugaban shawarar ya yi amfani da haƙƙoƙinsa domin a yi masa hukunci daidai da yadda ake yi wa kowane mutum da ke gaban kotu. Kuma shugaban ya amince da shawarar da muka ba shi."
Shari'ar dai ta fi mayar da hankali ne kan ko hukumomin Amurka da suka haɗa da Ma'aikatar Shari'a (DOJ) da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) da kuma Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi (DEA) za su fitar da wasu bayanai da takardun da suka shafi bincike da shari'o'in da aka yi a baya, waɗanda suka zama abin muhawara a siyasar Najeriya da ta Amurka.
Masu goyon bayan shugaban sun yi iƙirarin cewa yunƙurin neman a fitar da takardun yana da alaƙa da siyasa, yayin da masu sukar sa ke cewa ya kamata a bayyana su ga jama'a domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Sai dai Carmichael ya jaddada cewa batun yana gaban kotu, kuma hukuncin ƙarshe yana hannun alƙalin da ke sauraron shari'ar.
"Kamar yadda aka saba, alƙali ne zai yanke hukunci kan sakamakon shari'ar," a cewar lauyan.
Ya ƙara da cewa: "A matsayina na lauyan shugaban, muna da kyakkyawar fata cewa kotun za ta yi masa adalci, kuma za a kammala wannan shari'a cikin lokacin da ya dace."
Me Greenspan ke buƙata game da Tinubu?
Buƙatun da Greenspan ya gabatar sun haɗa da cikakken fayil ɗin da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ke da shi kan Tinubu, da kuma bayanan tambayoyi da aka yi wa mutane da ke cikin takardar FBI mai suna Form 302, waɗanda suka shafi lokacin tsakanin shekarun 1992 da 1993.
Har ila yau, shari'ar ta shafi wasu takardu da ake dangantawa da shari'ar ƙwace kuɗaɗe ta farar hula da aka yi a Amurka a shekara ta 1993, wadda ta shafi kimanin dala 460,000 da ake dangantawa da Tinubu.
Sai dai tawagar lauyoyin Shugaba Tinubu, ciki har da Chris Carmichael, ta kafa hujja a gaban kotu cewa fitar da waɗannan takardu na iya tauye masa haƙƙinsa na sirri, bisa ga wata takardar kotu mai shafuka 16 da kafofin yaɗa labarai suka gani.
A cewar ɗaya daga cikin takardun:
"Game da shari'ar ƙwace kadarorin ta 1993, takardun da aka gabatar a lokacin ba su nuna cikakkun bayanai kan wani binciken aikata laifi da aka yi wa Tinubu ko kuma sakamakon irin wannan bincike ba. Baya ga zato da zargi, mai shigar da ƙarar bai nuna wata takardar da ke ɗauke da cikakkun bayanai kan wani binciken gwamnati ko sakamakonsa a kan Tinubu ba."
Takardar ta ƙara da cewa: "Takardun da aka gabatar a lokacin shari'ar ba su bayyana cikakken bayani kan duk wani binciken aikata laifi ko sakamakonsa da ya shafi wanda ake ƙarar ba. Baya ga hasashe da zargi, mai shigar da ƙarar bai nuna wata takardar da ke ɗauke da bayanan bincike ko sakamakon binciken gwamnati a kansa ba."
Haka kuma takardar ta ƙara da cewa: "Kodayake an riga an bayyana wasu bayanai a lokacin shari'ar ƙwace kadarorin, wanda ake ƙara har yanzu yana da haƙƙin kare sirrinsa dangane da yiwuwar fitar da bayanan binciken da mai ƙarar ke nema."
Me cibiyar Von Batten-Montague-York ta ce?
Wata cibiyar bayar da shawarwari kan manufofi da kuma aikin rajin neman goyon baya da ke Amurka, Von Batten-Montague-York, ta yi zargin cewa shugaban Najeriya Bola Tinubu na ƙoƙarin hana fitar da wasu bayanai da take dangantawa da zarge-zargen safarar miyagun ƙwayoyi.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X da aka tabbatar da sahihancinsa ranar Asabar, cibiyar ta ce shugaban ya roƙi kotu ta umarci hukumomin Amurka kada su fitar da takardun.
A cewar cibiyar, Tinubu ya danganta buƙatar tasa da haƙƙinsa na kare bayanan sirrinsa.
A ranar Lahadi kuma, cibiyar ta ce Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) da Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi (DEA) sun miƙa wa kotu wasu sabbin takardu da suka shafi bayanan da ake zargin suna da alaƙa da binciken safarar hodar ibilis da ya shafi Shugaba Tinubu.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, cibiyar ta ce:
"Abin da ya ba mu mamaki shi ne mun gano cewa binciken da FBI ta gudanar kan bayanan da suka shafi Tinubu ya samar da shafuka 399 na takardu masu alaƙa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sanarwar ta ƙara da cewa takardun sun haɗa da bayanan da suka shafi binciken safarar miyagun ƙwayoyi, ciki har da gwajin hodar ibilis da aka gano da sayen miyagun ƙwayoyi da jami'ai suka gudanar ta hannun wani da ke ba da haɗin kai ga masu bincike.
''Da bayanan masu ba da labarin sirri da ayyukan babban alƙalin bincike da rahotanni da tarurrukan masu gabatar da ƙara da sa ido da binciken sirri da ƙwace kuɗaɗe da sammacin ƙwace asusun banki da bayanan binciken laifuka na Hukumar Haraji ta Amurka (IRS) da kuma haɗin gwiwar bincike tsakanin ƙasashe."
Sai dai har yanzu batun yana gaban kotu, kuma ba a yanke hukunci kan buƙatar fitar da waɗannan bayanai ba.







