Adadin waɗanda suka kamu da cutar Ebola a Kongo ya zarta 10,000

Asalin hoton, Getty Images
Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) ya haura 10,000, a cewar sabon rahoton kididdigar annobar da hukumomin lafiya na ƙasar suka fitar.
Rahoton, wanda Cibiyar Kula da Lafiyar Jama'a ta Ƙasa (INSP) ta wallafa, ya nuna cewa an samu sabbin mutum 96 da aka tabbatar sun kamu da cutar.
Jihar North Kivu ce ta fi yawan sabbin masu kamuwa da cutar inda ta ke da mutum 58, sai lardin Ituri mai mutum 32, yayin da yankin Tshopo ke da mutum shida.
Sabbin alkaluman sun nuna cewa jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a yayin annobar Ebola ta 17 da ƙasar ke fuskanta yanzu ta kai 10,060.
Mahukuntan lafiya sun ce mutum 4,887 sun mutu bayan kamuwa da cutar nau'in Bundibugyo, yayin da marasa lafiya 2,684 suka warke.
Haka kuma an sallami 14 a ranar 25 ga Oktoba bayan gwaje-gwaje biyu da aka yi musu sun tabbatar ba su ɗauke da cutar.
Hukumomin lafiya sun ce alƙaluman na nuna muhimmancin gano masu ɗauke da cutar da wuri tare da tabbatar da bin ƙa'idojin jana'iza cikin aminci domin daƙile yaɗuwar cutar.
Ko da yake North Kivu ce ta fi samun sabbin masu kamuwa da cutar a wannan lokaci, har yanzu Ituri ce yankin da annobar ta fi yi wa illa, inda take da kusan kashi 72 cikin ɗari na dukkan waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar tun bayan fara barkewar annobar.




















