Gaskiya ne tabar Shisha ba ta da hadari?

Shan wannan taba mai kanshin gaske na kara karbuwa a wurin jama'a, amma mafi yawan wadanda suke shanta ba su san hadarin da ke tattare da hakan ba.
Claudia Hammond ta bincika mana.
Za ka iya kiranta Shisha a Masar da Sudan, a Turkiyya da Syria Nargile ake ce mata, amma a Indiya da Hookah aka san ta.
Za ka ga an yi dan kurtun shanta wani da laka wani da karfe ko kuma roba, amma dai duk aikinsu daya ne, yadda za ka shaki hayakin tabar mai kanshi wanda yake ratsowa ta ruwa.
Watakila kai kasan ta ne kawai da sunan Hubble-bubble kamar yadda hayakin ke bulbulowa ta cikin ruwan ya biyo mesa ya kare a bakinka kafin ka fitar da shi ta hanci da bakin.
Shan wannan taba ta ruwa abu ne da ake ganin ba shi da wata illa, wanda kuma ke sa nishadi da hutu.
Yanzu dai mutane ne da dama suke cin moriyar wannan taba wadda ke tashe a Indiya da Gabas ta tsakiya inda aka ce daga nan ta samo asali.

A Gabas ta tsakiya yayin ya ratsa har tsakanin 'yan yara maza da mata da ma manyan mata wadanda yawancinsu ba sa shan taba.
Wannan yayi yanzu ya kai har ga kasashen Turai da Brazil da kuma Amurka inda za ka ga shagunan shan wannan taba mai zamani.
Idan na kama hanyar zuwa gidana daga ofis a Landan sai na ratsa ta wani titi da zan ga ayarin mutane daban-daban a shaguna hayaki mai kanshin zuma na Shisha ya turnuke su.
A Amurka an bude shagunan Shisha da dama a garuruwan da ake da manyan makarantu, kuma wani bincike da aka yi ya nuna akalla kashi daya bisa biyar na daliban Amurka sun taba shanta.
A kasashe da dama ana ganin wannan taba ba ta da illa saboda haka ma ba a sanya ta cikin dokar da ta shafi shan taba a wuraren jama'a ba.
To amma fa magana ko tunanin cewa wannan taba ba ta cutarwa wata almara ce kawai.
Hayaki a kan ruwa
Daya daga cikin rashin fahimtar da ake yi mata shi ne hadarin cutukan taba ya ragu saboda ruwa ya tsaftace hayakin a lokacin da yake ratsowa ta cikinsa.
Amma kuma an manta da asalin hayakin shi kansa wanda kake sha.

Idan ka duba za ka ga ai hayakin da kake sha ba na tabar ba ne kadai har da gawayin da ke kona tabar, wanda shi kuma gawayi yana dauke da wasu sinadarai masu hadari ga lafiya.
Wadannan sinadarai sun hada da na kwalta da na hayaki mai guba irin wanda masana'antu da na'urori kamar su mota da babur ke fitarwa.
Ita kuwa rariyar auduga ko ta roba da ke bakin wasu nau'in mesar da mutum ke zukar hayakin duk da cewa wasu na ganin tana rage yawan cutar da ke hayakin, hukumar lafiya ta duniya ta ce babu wata sheda da ta tabbatar da hakan.
Hadarin da ba a sani ba:
Gaskiya ne sanyaya hayakin da ruwan yake yi hakan yana rage mata hadari ta zama ba ta kai kamar taba cutarwa ba?
E! Gaskiya ne hakan zai iya sa mutum ya shaki hayakin da bai kai na taba hadari ba, to amma ba a la'akari da kuma yawan hayakin da mutum yake zuka?
Yawanci idan mutum ya zauna shan Shisha yana kaiwa akalla minti 20 zuwa sa'a daya.
To idan muka duba maimakon mutum ya yi zuka takwas zuwa 12 a karan taba daya, a Shisha yana zuka 50 zuwa 200 a zama daya.
Wannan idan muka duba za mu ga kamar daidai yake da mutumin da taba ta zamar masa jiki wanda da ya gama da wannan sai ya sake kunna wata.
Idan mutum ya kai sa'a daya yana shan Shisha zai zuki hayaki daidai da sau 100 zuwa 200 na yawan hayakin da mai shan taba kara daya yake zuka, wanda na san mutane da yawa za su yi mamaki.
Wani bincike da hukumar yaki da cutukan zuciya ta Birtaniya ta gudanar ya nuna cewa kashi 84 cikin dari na mutanen da aka tambaya game da yawan wannan hayaki da ake zuka a Shisha suna ganin ya kai na daidai da karan taba 10 ko kusa da haka.
A wani nazari da aka yi a Florida ta Amurka, an gudanar da bincike na yawan sinadarin hayaki mai guba (carbon monoxide) da ke cikin jinin mutanen da suka fito daga wani shago da ake shan Shisha da taba sigari.
A binciken an ga yawan sinadarin wannan hayakin da yake cikin jikin wadanda suka sha Shisha ya linka na wadanda suka sha taba sigari sau uku.
Wasunsu ma sun ce suna jin kamar sun bugu wanda wannan alamu ne in ji masu binciken na farko-farkon kamuwa da gubar hayaki mai guba.
To amma me muka sani game da hadarin shan Shisha a can gaba?
A nan za a iya cewa kimiyyar ba ta kammalu ba, domin irin nazari mai zurfi da aka yi a kan illolin taba sigari ba a yi shi ba a kan Shisha.
Masu bincike sun yarda cewa duk wata shaida da ake da ita ba cikakkiya ba ce, amma dai suna ganin masu shan Shisha din na iya gamuwa da hadarin cutukan zuciya da na daji da kuma kamuwa da bukatar shan sinadarin nikotin (nicotine) a ko da yaushe.
Shugaban sashen tiyatar zuciya a babban asibitin kasa na Saudi Arabia, National Guard Health Affairs, Farfesa Hani Najm, ya sheda min a wata tattaunawa cewa yana fargaba shan tabar Shisha zai iya kara yawan masu cutukan zuciya a kasashen yankin Gabas ta tsakiya.
To daga yanzu dai ka kwana da sanin wani abu daya idan kana shan Shisha ko Nargile ko kuma Hubble bubble, ba shakka tana da kanshi mai dadi amma maganar cewa ba ta da illa wannan shaci-fadi ne kawai.
Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan <link type="page"><caption> Shisha pipes: Is smoking them really harmless?</caption><url href="http://www.bbc.com/future/story/20120403-smoking-hubble-bubble-is-harmless" platform="highweb"/></link>
























