Abubuwa biyu da za su iya tantance wanda zai lashen zaɓen Najeriya na 2027

Atiku Abubakar da Bola Tinubu da Peter Obi

Asalin hoton, X/Multiple

    • Marubuci, Abubakar Maccido
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
    • Aiko rahoto daga, Kano, Nigeria
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da jam'iyyun siyasa da ƴan takara ke ciga da zage damtse wajen shirya wa babban zaɓen Najeriya na 2027, akwai abubuwan da masu kaɗa ƙuri'a za su fi la'akari da su wajen zaɓen wanda zai zama shugaban ƙasa.

Tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi, rashin lantarki, matsalolin kiwon lafiya da ilimi da kuma shugabanci na daga cikin abubuwan da ƴan Najeriya ke yawan magana a kansu.

A baya-bayan nan batun tallafin man fetur ya haifar da muhawara a Najeriya bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya ce zai mayar da tallafin idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

Amma wadanne abubuwa ne za su fi jan hankalin masu kada ƙuri'a gabanin zaɓen 2027?

Women casting their votes

Asalin hoton, MICHELE SPATARI VIA GETTY IMAGES

Tsadar rayuwa

Wani masanin siyasa a Kano, Sani Bala ya faɗa wa BBC cewa abin da ƴan Najeriya za su yi la'akari da shi sosai game da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 shi ne tsadar rayuwa.

Bala ya ce ganin yadda ƴan Najeriya ke cikin matsin rayuwa, za su duba abin da ƴan takara za su iya yi musu game da sassauta tsadar rayuwa.

Lokacin da aka tambaye shi game da abin da ya fi muhimmanci ga masu kaɗa ƙuri'a tsakanin matsalar tsaro da matsin rayuwa, sai ya ce matsin rayuwa na ƙuntata wa ƴan Najeriya a kowane lokaci.

"Tsadar rayuwa ce babban abin da ke addabar ƴan Najeriya, kasancewar komai ya yi tsada. Mutane da dama na shan wahala kan yadda za su ciyar da iyalansu saboda ƙuncin tattalin arziƙi," in ji shi.

Ya yi bayani kan cewa tashin farashin kayan masarufi ya sanya rayuwa ta yi wahala ga mutane da dama.

Ya ce masu kaɗa ƙuri'a za su mayar da hankali kan ƴan takara da za su bunƙasa tattalin arziƙin al'umma a maimakon waɗanda za su riƙa yi musu alƙawarran da aka saba ji.

Matsalar tsaro

Sani Bala ya ce duk da rashin tsaro babbar matsala ce, ya kamata ƴan siyasa su tabbatar wa mutane abin da za su yi wajen magance matsalar.

"Rashin tsaro babbar matsala ce a ƙasar, kuma duk ɗan siyasar da ya ce ga lokacin da zai magance matsalar, to da alama ba da gaske yake yi ba. Mun ga irin haka a baya, inda wasu ƴansiyasa suka yi alƙawarin magance matsalar a cikin wani lokaci amma suka gaza," in ji shi.

Bala ya ce ƴan siyasa sun sha yin alƙawarin magance matsalar tsaro, to amma har yanzu matsalar na addabar sassa daban-daban na ƙasar.

Ya shawarci masu kaɗa ƙuri'a kada su tsaya sauraran alƙawurra na fatar baki, ya kamata su duba su gani ko ƴan takaran na da kyakkyawan tsarin matsalolin.

Sai dai Bala ya ce magance matsalar tsaro ba abu ne da ya rataya a wuyan ƴan siyasa kawai ba.

"A ɗaya ɓangaren ya kamata a sani cewa kowa na da rawar da zai taka wajen magance matsalar tsaro, ba ƴan siyasa kawai ba," in ji shi.

Ya ce wannan ya sanya ya kamata mutane su yi taka-tsantsan da ƴan siyasa waɗanda suke yi musu alƙawarin kawar da tsaro cikin wani ƙanƙanin lokaci.

Yadda ƴan Najeriya za su gane ƴan takara nagari

Sani Bala ya ce ya kamata al'umma su tambayi ƴan takara matakan da za su ɗauka dalla-dalla kan yadda suka yi shirin cika alƙawuran da suka ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ya ce ya kamata ƴan Najeriya su yi binciken asalin kowane ɗan takara da za su zaɓa.

"Duk lokacin da ɗan takara ya ce zai magance wata matsala, ya kamata ku tambaye shi: ta yaya za ka magance matsalar?" in ji shi.

Bala ya ce yin irin wadannan tambayoyi za su taimaka wa masu kada ƙuri'a su bambance tsakanin ƴan takara da suka shirya da kuma wadanda suke yin alƙawari domin lashe zaɓe kawai.

Masanin siyasar ya kuma shawarci ƴan Najeriya su duba tarihin ƴan takara, musamman waɗanda suka riƙe muƙaman gwamnati a baya.

"Yana da kyau ƴan Najeriya su duba ayyukan da ƴan takara suka yi a lokacin da suka riƙe wani muƙami a baya, su ga mene ne ya yi wa jiharsa da kuma ƙasar lokacin da yake riƙe da mukami," in ji shi.

Ya bayyana cewa abin da mutum ya yi a baya na da muhimmanci wajen tantance ɗan takarar da ya kamata a sake bai wa dama a gaba.

Haka nan ya shawarci mutane su duba ilimi da kuma ƙwarewar ƴan siyasa.

"Idan wani ɗan takara ya zargi wani ɗan takarar da gazawa, ya kamata mutane su tambaye shi, wace ƙwarewa yake da ita a wannan fanni kuma me ya yi a baya game da wannan matsala," in ji shi.

Yana ganin cewa hakan zai sanya yaƙin neman zaɓe ya mayar da hankali kan matsaloli, da manufofi da kuma abin da mutum ya aikata a baya a maimakon cin fuska ko kushe abokin hamayya.

Ƴan takara su san matsalar al'umma

Sani Bala ya yi misali da tambayoyin da al'umma za su yi wa ɗan takara idan ya ce zai bunƙasa ɓangaren ilimi.

Ya ce idan ɗan takara ya ce zai gyara ɓangaren ilimi akwai tambayoyin da al'umma za su iya yi masa.

"Misali, idan mutum zai yi takarar gwamna, kuma ya yi alƙawarin magance matsalar ilimi, ku tambaye shi makarantu nawa ne a jihar, ɗalibai nawa ne kuma malamai nawa? Da kuma matakan da zai bi wajen magance matsalar.

"Mafi yawan ƴan takara ba za su iya amsa wannan tambayar ba," in ji shi.

Ya bayyana cewa duk wani ɗan takara da ke da shirin magance matsala, to ya kamata a ce ya san girma da munin matsalar da kuma hanyoyin da za a iya bi wajen magance ta.

Bala ya ce ƴan ƙasa na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen gyara harkar siyasa ta hanyar zaɓen mutane nagari.

Ya ce bai kamata mutane su zaɓi ƴan takara kawai saboda jam'iyya ko alƙawura na fatan baki ba.

A maimakon hakan ya shawarci mutane su yi bincike kan ƴan takara, da duba ayyukan da suka yi a baya da kuma tambayar su yadda za su magance matsalolin da ke addabar al'umma.

"Shi ya sa yake da kyau mutane su san mutanen da za su zaɓa da kuma yadda za su magance matsalolin al'umma," in ji Bala.