Takarar Ballon d'Or: Fafatawa ta yi zafi a neman kyautar ƙwallon ƙafa mafi girma

Asalin hoton, Getty Images
Kamar yanzu ne Ousmane Dembele ya lashe kambun a bara, sai gashi har an fara takarar lashe kyautar Ballon d'Or ta bana, kuma tuni an kammala kaɗa ƙuri'ar zaben gwarzon bana da ake sa ran sanar da shi a ranar Litinin a Landan.
Wane ne ya cancanci lashe kyautar Ballon d'Or 2026? Shekarar da aka gudanar da gasar Kofin Duniya ce, inda a wasu lokuta muhawarar ta wuce batun waɗanne ƴan wasa za su jagoranci ƙasashensu zuwa lashe kofin duniya, ta koma wane ne zai lashe babbar kyautar tamaula ta dan wasa daya a dunuya.
"A kowacce rana ana ta tattauna kan batun Ballon d'Or," in ji masanin ƙwallon kafar Turai Guillem Balague a shirin podcast na Euro Leagues na BBC Sport.
Masu horarwa da daraktocin wasanni sun riƙa yabon ƴan wasansu, tare da tambayar dalilin da ya sa wasu daga cikin fitattu ba sa cikin jerin 'yan wasa 30 masu takara da aka bayyana.
Deco ya bayyana rashin saka ƴan wasan Barcelona kamar Raphinha da Pedri a matsayin "babban abin kunya", amma ya goyi bayan da Lamine Yamal yana cikinsu, wanda yake cewa ya fi kowa damar lashe kyautar bana, saboda rawar da ya taka a 2026. A cewarsa, ba saboda ɗan wasan Barcelona ba ne, sai dai "saboda ina son ƙwallon ƙafa."
Manyan ƴan wasa sun yi ta hira da kafafen yaɗa labarai. Shi ma Lamine Yamal ya ce ba zai "roƙi komai ba", bayan da ya ce a bara mafarkinsa shi ne "lashe kyautar sau da yawa", amma ya yi nuni da cewa bai kamata a ba wa wanda ya fi cin ƙwallaye kawai kyautar Ballon d'Or ba.
Kocin Paris St-Germain, Luis Enrique ya amsa cewa ya "gaji da maganar Ballon d'Or", ko da yake da 'yan wasan PSG 10 a jerin sunayen masu takara, watakila yana son kauce wa muhawarar ce, saboda yawan tambayarsa da ake kan kyautar.
Dembele da Khvicha Kvaratskhelia sun yi ta yabon juna a wata hira da BBC Sport.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Za mu iya raba kyautar gida biyu," Dembele ya yi barkwancin cewa, "Gaskiya ya cancance ta, kakar wasan da ya yi ta musamman ce."
Kvaratskhelia ya mayar da martani da cewa: "Tabbas shi ne ya cancanta!"
An kuma gudanar da wani kamfen mai suna "Kvara d'Or" a Georgia domin nuna goyon baya ga fitaccen ɗan wasan ƙasar.
"Ina ganin ga manyan ƙasashe yana da wuya su fahimci abin da hakan ke nufi ga ƙaramar ƙasa," in ji ɗan wasan na PSG.
Kylian Mbappe, wanda kocin Real Madrid, Jose Mourinho ya kwatanta da Ronaldo na asali, bai yi ɓoye-ɓoye ba wajen nuna burinsa na lashe kyautar a karon farko.
"Kullum ina ganin ni ne na fi kowa kyau a fannin taka leda, amma kowa na da ra'ayinsa," in ji ɗan wasan Faransa, wanda yanzu shi ne wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin Kofin Duniya, wato Kylian Mbappe.
"Tabbas, wannan shekara na iya zama mai kyau a gare ni wajen lashe Ballon d'Or, amma 'yan jarida ne suke kada kuri'a."
Haƙiƙa tun bayan da aka daina tsarin da kyaftin-kyaftin da masu horar da ƙasashe ke kaɗa ƙuri'a a shekarar 2015, ana zaɓen wanda zai yi nasara ne daga jerin ƴan wasa 30 da France Football da L'Equipe suka tsara, inda ɗan jarida ɗaya daga kowace ƙasa cikin ƙasashe 100 mafi matsayi a jadawalin Fifa ke kada kuri'a.
An riga an zaɓi wanda ya yi nasara, ranar Litinin ake jira domin bayyana gwarzon dan ƙwallon ƙafa na duniya na 2026.
Messi da Ronaldo da kakafen sada zumunta

Asalin hoton, Getty Images
James Kirkham, wani masanin dabarun tallata harkar wasanni wanda ya yi aiki tare da manyan ƙungiyoyi da ƴan wasa, ciki har da Harry Kane, ya ce shirye-shiryen da ake yi kafin bikin sun yi kama da yaƙin neman zaɓe.
Wannan ƙoƙarin neman goyon baya ba ya birge kowa. Max Eberl, mamban kwamitin kula da harkokin wasanni na Bayern Munich, yana goyon bayan Kane da Michael Olise, amma ya ce fitattun ƴan wasa "su ne waɗanda ba sa buƙatar gudanar da wani yaƙin neman zaɓe", domin rawar da suka taka a shekarar ta isa shaida.
A gefe guda kuma, Jean-Pierre Papin, ɗan ƙasar Faransa, wanda ya lashe kyautar a shekarar 1991, ya shaida wa gidan talabijin na Faransa cewa: "Ina matuƙar son Kylian, domin yana kafa tarihi a koda yaushe. Amma akwai lokacin da komai ya zama ni ne ake magana a kan batun taka leda a duniya."
Mbappe ma ya yi wani tsokaci mai jan hankali, inda ya yi batun kan yadda Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suka mamaye kyautar a baya. Su biyun sun lashe kyautar sau 13 a tsakaninsu cikin shekara 15 tsakanin 2008 zuwa 2023.
"A yau komai yana tafiya cikin sauri da sauyi sosai," in ji tsohon babban jami'in gudanarwa kuma daraktan wasanni na AC Milan, Ariedo Braida, wanda ya shaida lokacin da ƙungiyar take da ƴan wasa bakwai da suka lashe kyautar daga Ruud Gullit zuwa Marco van Basten da ya ɗauki uku rigis da kuma George Weah da Andriy Shevchenko da kuma Kaka.
"Magoya baya a yanzu suna bin mutum, wato ƴan wasa, maimakon ƙungiya kamar yadda aka yi a baya. Wannan wani abu ne da ya yaɗu sosai, kuma muna ganinsa har ma a siyasa.
"A da, za ka kasance magoyin bayan Milan ne kuma ka tafi kallon Milan. Yanzu kuwa komai kai tsaye ne, kenan za ka iya kallon Gasar Zakarun Turai kana iya kallon dukkan manyan taurari nan take, ka kuma fayyace kwazon kowa.

Asalin hoton, Getty Images
Bajintar Messi da Ronaldo, tare da mabiya masu tsananin goyon baya a shafukan sada zumunta, sun kuma ƙara jaddada muhimmancin tarihin nasarorin mutum ɗaya, a tsakanin magoya baya, kafafen yaɗa labarai da kuma 'yan wasan da suka taso suna mafarkin kwaikwayon su.
"Za ka iya cewa muna cikin wani lokaci mai ban sha'awa saboda kusan tsawon shekaru 15 ana kallon lamarin a matsayin Messi da Ronaldo, kuma yanzu da alama an buɗe fagen ga kowa. Yanayin ya sauya yanzu," in ji Kirkham.
"Hayaniyar da ake yi a shafukan sada zumunta tana da ƙarfi sosai, ba ta yankewa kuma tana mamaye komai. Kowane mai goyon baya na da kishirwa mara ƙarewa, ana tattauna kowane batu tare da mayar da martani a kai, amma kana kuma da wannan tasirin da ke yaɗuwa a ƙananan sassan kafafen yaɗa labarai a kan kowace dandali."
Gajerun bidiyoyi na yaɗuwa cikin sauri, ko saboda wata kyakkyawar ƙwallo, wata bajintar fasaha, ko wani gagarumin gudu da ƙwallo, amma haka ma ra'ayoyi kan yi yawo.
"Yanzu ma kalma guda da aka faɗa a wani shiri na iya zama sakonnin X, masu ƙirƙirar abun ciki da tsoffin 'yan wasa su mayar da martani a bidiyoyi a reels da shorts da stories, sannan hakan ya koma cikin shirye-shiryen rediyo da talabijin," in ji Kirkham.
"Dukkan tsarin ne gaba ɗaya, yadda yake ƙara ƙarfi a waɗannan wurare da dandamali daban-daban, sannan ya samar da sabbin labarai da ruwayoyi.
"Babu wanda yake yin wani abu ba daidai ba, kowa na ƙirƙirar abin da yake ganin zai yi daidai da masu sauraronsa. Amma idan aka haɗa komai tare, hakan ya zama wata babbar na'ura mai ƙarfi da ke samar da abubuwan da za su tallafa wa ɗan wasa ko suƙe shi, ko mene ne lamarin."
Braida, wanda yake tare da Barcelona lokacin da Messi ya lashe kyautar ta 2015, ya amince da hakan.
"A yau, fitowa fili a kafafen yaɗa labarai abu ne mai matuƙar muhimmanci. Tun bayan bayyanar shafukan sada zumunta, duniya ta canza ƙwarai idan aka kwatanta da zamanina.
"An samu sauyi a matakin duniya baki ɗaya, kuma a yau muna rayuwa ne a cikin wata ƙaramar ƙauyen duniya, saboda da intanet za ka iya isa ko'ina a lokaci guda."
Abin da hakan ke nufi
Michael Owen ya ba da labari kan yadda kocin Liverpool Gerard Houllier ya kira shi domin sanar da shi cewa ya lashe kyautar a shekarar 2001, amma matashin mai shekara 22 a lokacin bai ma san menene Ballon d'Or ba.
Shi ne ɗan wasa na farko daga ƙungiyar Ingila da ya lashe kyautar tun bayan George Best na Manchester United a shekarar 1968, a wani lokaci da kungiyoyin Italiya da Sifaniya da Jamus suka mamaye kyautar a wancan lokacin.
Tun daga lokacin da aka ƙirƙiri bayar da kyautar daga 1956 har zuwa 1995 da Jorge Weah ya zama ɗan wasan Afirka na farko kuma har yanzu shi kaɗai ne daga nahiyar da ya taba lashe ta, ƴan wasan Turai ne kawai suke cancanci shiga takara.
Sai a 2007 ne kyautar ta zama ta duniya baki daya, inda aka bude wa 'yan wasa daga kowacce kungiya damar shiga, ba wai kawai wadanda ke wakiltar kungiyoyin Turai ba.
Ga mutum irin kyaftin din tawagar Ingila, Kane, wanda ke fatan zama ɗan Ingila na farko da zai lashe kyautar cikin shekara 25 kuma na biyar gaba ɗaya a tarihin ƙasar, martabar kyautar na da girma matuƙa, musamman ganin cewa za a gudanar da bikin a Landan domin cika shekara 70 da Stanley Matthews ya lashe kyautar farko.
Kane ya yi nasa ɓangaren na tattaunawa da kafafen yaɗa labarai a baya-bayan nan, amma wasu kamar Rio Ferdinand a shafukan sada zumunta na Bayern na hukuma sun yi masa kamfen.
Haka kuma Bayern na fatan ɗan ƙasar Ingila zai zama na farko da zai lashe kyautar tun bayan nasarar Karl-Heinz Rummenigge wanda ya dauka karo biyu a jere a shekarar 1981.
Tun bayan Matthias Sammer na Borussia Dortmund shekara 30 da suka gabata ne kawai kyautar ta taba komawa Bundesliga.
Bayern za ta kuma tuna da lamarin Robert Lewandowski, wanda mutane da dama suka yi hasashen shi ne zai lashe kyautar a shekarar 2020, bayan ya zura kwallaye da adadi mai ban mamaki, yayin da kungiyar Bavarians ta lashe dukkan kofuna shida da ta yi takara a kansu, ciki har da Champions League, kafin a soke bikin saboda annobar Covid-19.
Ɗan wasan Poland din, wanda ya zo na biyu bayan Messi a kakar da ta biyo baya, ya shaida wa BBC Sport a bara cewa kyautar ta zama "wani ɓangare na ƙwallon ƙafa, wani ɓangare kuma na siyasa", kuma ta fi mayar da hankali kan kasuwanci fiye da kyautar The Best Fifa Men's Player.
Rashin samun Ballon d'Or na iya barin rauni mai zurfi a zuciyar dan wasa. Franck Ribery ya ce ya ji tamkar "an yi masa fashi" lokacin da ya sha kaye a hannun Ronaldo a shekarar 2013.
Real Madrid ta kaurace wa bikin shekarar 2024, bayan ta samu labarin cewa dan wasan Manchester City, Rodri ne zai lashe kyautar maimakon Vinicius Junior.





























