Muhimman abubuwa 5 da Tinubu da muƙarrabansa suka faɗa a Kaduna

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da yakin neman zaɓen wa’adi na biyu na shekarar 2027 a Kaduna - daya daga cikin jihohin da ya fadi zabe a 2023 kuma ta uku a yawan masu kada kuri’a - inda manyan jagororin APC daga Arewacin Najeriya da takwarorinsu na kudu suka hallara domin bayyana nasarorin da suke ganin gwamnatin ta samu a tsawon kusan shekara hudu da kuma neman goyon bayan masu zaɓe.
Taron ya samu halartar jiga-jigan jam'iyyar mai mulki, da gwamnoni, da shugabannin siyasa da magoya bayan APC daga sassa daban-daban na kasar.
Tinubu na neman wa'adin mulkin ƙasar a zagaye na biyu, inda zai fafata da ƴan takara da dama, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC, da Peter Obi na jam'iyyar NDC.
Daga cikin abubuwan da suka ja hankali a game da yaƙin zaɓen, akwai zaɓen jihar Kaduna domin ƙaddamar da shi, jihar da tsohon gwamnanta Nasir El-Rufai, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tallata Tinubu a 2023 ke tsare a hannun hukumomin ƙasar duk da gudunmuwar da bayar a baya.
Taron Kaduna ya zama wani dandali da shugabannin APC suka yi amfani da shi wajen jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta samu nasarori musamman a fannonin tsaro, tituna, ilimi, noma da samar da ababen more rayuwa.
BBC ta yi nazarin yadda aka ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ma Shugaba Tinubu, sannan ta rairayo wasu muhimman abubuwan da aka faɗa faɗa a taron.
Ƴan hamayya ne suka jefa Najeriya cikin talauci - Tinubu

Asalin hoton, Getty Images
A nasa jawabin, Shugaba Bola Tinubu ya fara da gaisuwa cikin harshen Hausa ga dubban magoya bayan jam'iyyar APC da suka halarci taron, inda ya ce "sannunku da zuwa.
Daga nan ya mayar da hankali kan sukar da ƴan adawa ke yi wa gwamnatinsa dangane da matsalar tsadar rayuwa da yunwa.
A cewarsa, "ina jin masu adawa suna magana kan yunwa da talauci. Amma wa ya jawo su? Su ne suka haddasa talauci, su ne suka haddasa yunwa. Mu kuma muna ƙoƙarin kawar da su."
Shugaban ƙasar ya ce gwamnoninsu na jam'iyyar APC suna aiki domin inganta rayuwar jama'a.
Ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa: "Tallafin fetur ya zama tarihi. Ba za a ƙara yaudarar jama'a ba."
Tinubu ya zargi masu adawa da nuna fushi saboda sun gaza, sannan ya yi kira ga magoya bayan APC su zaɓi jam'iyyar daga sama har ƙasa a zaɓukan da ke gaba.
Wani abu da ya ja hankali a game da taron shi ne yadda Tinubu ya ƙaddamar da wani ɓangare na aikin titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano a filin taron.
Ba don Tinubu ba da Buhari bai zama shugaban ƙasa ba - Kashim

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da yake gabatar da nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce nasarar APC a Kaduna ta samo asali ne daga haɗin kai tsakanin al'ummomi daban-daban da ke jihar.
Ya ce a yau mutanen yankuna daban-daban na Kaduna suna kallon juna a matsayin ƴan'uwa, kuma wannan babbar nasara ce da APC ta samu.
Shettima ya ce gwamnati ta yi ƙoƙarin cika alƙawarin da ta ɗauka na mayar da Kaduna cibiyar ci gaba a Arewacin Najeriya.
Ya lissafa wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa a Arewa da suka haɗa da:
- Jami'ar Tarayya ta Federal University of Applied Sciences a Kachia.
- Jami'ar ilimi ta tarayya a Zariya.
- Samar da cibiyoyin koyon sana'o'i da ayyukan yi ga matasa.
- Ci gaba da aikin bututun iskar gas na AKK.
- Aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna.
- Aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.
- Aikin layin dogo zuwa Maradi.
Shettima ya kuma tuna irin rawar da Tinubu ya taka a siyasar Najeriya tun shekarun baya.
A cewarsa, Tinubu ya mara wa Atiku Abubakar baya lokacin da ya ke neman takara a ƙarƙashin Action Congress, sannan ya mara wa Nuhu Ribadu baya a 2011, kafin daga baya ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Muhammadu Buhari a zaɓukan 2015 da 2019.
"Wallahi, ba don gudunmuwar Tinubu ba, Buhari ba zai zama shugaban ƙasa ba," in ji Shettima.
Ya ƙara da cewa: "A Arewa ba a san mu da butulci ba. Ya kamata mu rama alherin da aka yi mana."
Tinubu ya cika mana alƙawari - Uba Sani

Asalin hoton, Getty Images
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya ce Shugaba Tinubu ya cika alƙawura biyu da ya ɗauka wa jihar tun kafin hawansa mulki.
Ya ce alƙawari na farko shi ne sake gina hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari mai tsawon kilomita 123 da ya ce an yi watsi da ita sama da shekara 40.
"Ka yi mana alƙawarin gyara hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, kuma yanzu an fara aikin bayan kasafta kuɗi naira biliyan 117. Mutanen Birnin Gwari suna godiya," in ji gwamnan.
Alƙawari na biyu kuwa, a cewarsa, shi ne inganta tsaro a hanyar Birnin Gwari da kewaye.
"Yanzu zan iya tabbatar maka cewa mutum zai iya zuwa Birnin Gwari ido rufe ba tare da rakiyar jami'an tsaro ba."
Gwamnan ya bayyana cewa lokacin da suka karɓi mulki a 2023, ƙananan hukumomi takwas na fama da matsalar rashin tsaro, lamarin da ya sa aka rufe makarantu sama da 300 da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko sama da 150.
Ya ce yanzu an sake buɗe dukkan waɗannan makarantu da cibiyoyin lafiya.
Uba Sani ya kuma tunatar da shugaban ƙasar wani alƙawari da ya cika na fara aikin hanyar Zariya-Soba-Panbegua, wadda ya ce al'ummar yankin suka daɗe suna jira tun shekara ta 2011.
"Tun a 2011 shugaban majalisar wakilai na yanzu yake neman a gyara hanyar, amma yanzu an fara aikin."
Haka kuma ya yaba masa kan zaɓar Kaduna a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da za a fara aikin layin dogo na cikin birni.
A cewarsa, an ware dala miliyan 865 domin aikin, yayin da kamfanin da ke aiwatar da shi ya samu kusan dala miliyan 300 a matsayin kuɗin fara aiki.
Uba Sani ya ce ya taɓa ganawa da shugaban ƙasar shekaru biyu da suka gabata domin nuna masa muhimmancin hanyar Abuja-Kaduna-Kano ga Arewa.
A cewarsa, Tinubu ya amince da sakin kuɗaɗen gyaran hanyar, kuma yanzu aikin ya kai kusan kashi 95 cikin 100 na kammaluwa.
Ya ce hanyar na haɗa jihohi 12 na Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas, sannan tana haɗa Arewa da Kudancin Najeriya.
Da ayyukan Tinubu za mu tallata shi - Yari
Shi ma darakta-janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce APC ba za ta dogara da alƙawura kaɗai ba wajen neman kuri'un jama'a, domin tana da ayyukan da za ta nuna.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu wahala amma masu muhimmanci wajen gyara tattalin arzikin ƙasar, ciki har da cire tallafin man fetur da sauye-sauye a tsarin canjin kuɗi.
Yari ya ce jam'iyyar za ta nuna nasarorin da ta samu a fannin kiwon lafiya, ilimi, ci gaban matasa, ababen more rayuwa da kuma shirye-shiryen tallafa wa marasa ƙarfi.
Ya kuma ce shugabannin gargajiya, malamai, limamai da sauran masu ruwa da tsaki a Arewa suna ci gaba da wayar da kan jama'a kan muhimmancin sake zaɓen Tinubu domin ci gaba da manufofin gwamnati.
Sai dai mafi jan hankali a jawabinsa shi ne lokacin da ya ce: "A Arewacin Najeriya, muna goyon bayan Bola Ahmed Tinubu kashi 101 cikin 100, kuma za ku gani a ranar zaɓe."





























